By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Hamas ta Bayyana Sunayen Isra’ilawa uku da za ta Saki Gobe Asabar
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Hamas ta Bayyana Sunayen Isra’ilawa uku da za ta Saki Gobe Asabar
News

Hamas ta Bayyana Sunayen Isra’ilawa uku da za ta Saki Gobe Asabar

Attajdid
Last updated: 2025/02/14 at 4:06 PM
Attajdid Published February 14, 2025
Share
SHARE

Bayanan hoto,Alexander Troufanov da Yair Horn da kuma Sagui Dekel-Chen duk suna cikin mutanen da mayaƙan Hamas suka kwasa daga Isra’ila a ranar da suka kai samame

 

Hamas ta saki sunayen mutum uku da take garkuwa da su waɗanda za ta saki gobe Asabar domin yin musaya da Falasɗinawan da Isra’ila ke riƙe da su a wani ɓangare na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

 

Hakan na zuwa ne bayan kwanakin da aka kwashe ana fargabar wargajewar yarjejeniyar.

 

Isra’ilawan da za a sakin su ne: Alexander Troufanov – ɗan Isra’ila mazaunin Rasha, da Yair Horn – ɗan Isra’ila mazaunin Argentina, da kuma Sagui Dekel-Chen – ɗan Isra’ila mazaunin Amurka.

 

Isra’ila ta bayyana cewa za ta ci gaba da ruwan wuta a kan Gaza idan ba a saki mutanen a kan lokaci ba.

 

Taƙaddama ta kaure ne bayan da Hamas ta yi barazanar dakatar da sakin mutanen na Isra’ila bayan zargin Isra’ilar da karya ƙa’idojin yarjejeniyar tsagaita wuta.

 

Tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar 19 ga watan Janairu, Hamas ta saki Isra’ilawa 16, da ƴan ƙasar Thailand biyar yayin da ita kuma Isra’ila ta saki Falasɗinawa 566 da take riƙe da su a gidajen yarinta.

 

Ana sa ran Hamas za ta saki ‘ƴan Isra’ila 33 da take garkuwa da su a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da ita kuma Isra’ila za ta saki Falasɗinawa 1,900.

 

Yaƙi ya turnuƙe a Gaza ne tun bayan da Hamas ta kai wani hari kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda mayaƙanta suka kashe kimanin mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu mutum 251.

 

Tun bayan wancan lokacin, ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce an kashe sama da mutum 48,230 sanadiyyar luguden wuta da Isra’ila ta riƙa yi a Gaza. BBC Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid February 14, 2025 February 14, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

‘Yan Sandan Najeriya Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga a Abuja

Attajdid Attajdid October 1, 2024
Kalubalen Zirga-Zirgar Ababan Hawa A Kano
Belgium ta bi sahun ƙasashe sama da 140 da suka amince da cin gashin kan Falasɗinu
Mutum Uku ke Magana da Yawuna Tinubu Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Ko ECOWAS za ta iya jure wa ƙalubalen da ke gabanta?
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?