By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Jam’iyyar NNPP ta Lashe Zaɓen Shugabannin ƙananan Hukumomin 44 da Kansiloli 484 Jihar Kano: Farfesa Malumfashi.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Jam’iyyar NNPP ta Lashe Zaɓen Shugabannin ƙananan Hukumomin 44 da Kansiloli 484 Jihar Kano: Farfesa Malumfashi.
News

Jam’iyyar NNPP ta Lashe Zaɓen Shugabannin ƙananan Hukumomin 44 da Kansiloli 484 Jihar Kano: Farfesa Malumfashi.

Attajdid
Last updated: 2024/10/27 at 10:58 AM
Attajdid Published October 27, 2024
Share
SHARE

Hukumar zaɓen Kano da ke arewacin Nijeriya (KANSIEC) ta sanar da ‘yan takarar jam’iyyar NNPP mai mulkin Jihar a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar.

 

Jam’iyyar ta NNPP ta cinye zaɓukan ƙananan hukumomi 44 da na kansiloli 484, a cewar shugaban hukumar zaɓe na jihar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi.

 

“Kamar yadda duniya ta gani, an yi wannan zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana tare da cikakkaiyar samun nasara…bisa ga sakamakon da wakilan hukumar zaɓe na ƙananan hukumomi suka miƙo mana, jam’iyyar NNPP ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli 484,” in ji Farfesa Malumfashi.

Ya ƙara da cewa jam’iyyu shida ne suka fafata a zaɓen.

Jam’iyyun su ne: Nigeria People Party (NNPP), Zenith Labour Party (ZLP) Accord Party (AP) National Rescue Movement (NRM), African Action Congress (AAC) da Action Alliance (AA).

 

Babbar jam’iyyar adawa a Jihar, APC, ta ƙaurace wa zaɓen.

Zaɓen dai ya fuskanci ƙalubale daban-daban domin kuwa Kotun Tarayyar Nijeriya ta haramta gudanar da shi bayan da ta ce wasu mambobin hukumar zaɓen ta Kano, ciki har da shugabanta Farfesa Malumfashi, ‘ya‘yan Jam’iyyar NNPP ne.

 

Sai dai kotun jihar Kano ta yi hukunci wanda ya ci karo da na tarayya inda ita kuma ta umarci hukumar zaɓen ta Kano da ta gudanar da zaɓen a ranar Asabar.

 

Ita kuwa rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta bi umarnin kotu, inda ta ƙaurace wa zaɓen.

 

Amma jami’an hukumar Hisbah da ‘yan Karota sun tabbatar da tsaro a rumfunan zaɓe.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid October 27, 2024 October 27, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Dangote: Yanboko An Ji Kunya. Tir!

Attajdid Attajdid September 15, 2024
NDLEA
Aljeriya ta Buƙaci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka
MAAIKATAN JINYA SUN JANYE YAJIN AIKIN YAU
AN SAMU CIMA MATSAYA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA KARIM LAMIDO
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?