- AN SAMU CIMA MATSAYA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA KARIM LAMIDO
Manoma da Makiyaya a garin Karim Lamido sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da juna yayin wani taron sulhu da jamiʼan tsaro suka yi da jagororin alʼummar yankin.
Wakilin Arewa Update, Muhammad Usamat Suleiman, ya ruwaito cewa an tura jamiʼan tsaron yan sanda, sojoji da jamiʼan Civil Defense da yan sa kai don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




