Netanyahu yana kara fuskatar matsil lamba daga cikin gida wadda hakan ya kawo aji ra’ayoyin yahudawa Kamar yadda 24 Channel na Isra’ila yakawo Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da ta nuna cewa kashi 52 cikin 100 na ‘yan Isra’ila sun yi imanin cewa Netanyahu ba shi da kwarewa wajen tafiyar da yakin, yayin da kashi 45% daga cikinsu suka yi imanin cewa Gallant ba ya gudanar da shi yadda ya kamata, baya ga 38% wadanda suka yi imanin cewa Halevy ba shi da kwarewa a wannan yaki.
A tashar talabijin ta Isra’ila 12 ta bayar da rahoton wani kuri’ar jin ra’ayin jama’a kashi 60% na ‘yan Isra’ila sun yi imanin cewa kulla yarjejeniya ya fi muhimmanci fiye da kasancewa a cikin Philadelphia axis 61% na Isra’ila ba su amince da cewa gwamnati na yin iyakar kokarinta don dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Tashar Isra’ila ta 12 ta labartomana cewa Sojojin saman sun kai hare-hare masu yawa kan harba makamai masu linzami a kudancin Labanon.
Yawan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kudancin Lebanon ya karu zuwa sama da 20, kuma an sake sabunta hare-haren a wadannan lokutan ma.
Wani tsohon jami’in Shin Bet ya gaya wa Channel I24 ta Isra’ila “Ban yi imani da shugabannin tsarin tsaro na Isra’ila ba dole ne su dauki alhakin harin na Oktoba 7” kuma ya yi murabus daga matsayinsa daga Gaza a daren da aka kai harin.
At-tajdid News.




