By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe.
News

Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe.

Attajdid
Last updated: 2025/09/13 at 5:56 PM
Attajdid Published September 13, 2025
Share
SHARE

Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe.

 

Yayin mika kayan tallafin a fadar dagacin yankin a ranar Laraba, Sakataren gudanarwa na SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna, ya ce gwamna Inuwa Yahaya ne ya amince da bayar da kayan tallafin, wadanda suka kunshi kayan abinci da na masarufi.

 

Kayan da aka raba sun hada da buhunan shinkafa, taliya, tabarma, zannuwa, da tufafin yara, da sauransu.

 

A cikin jawabinsa ga waɗanda al’amarin ya shafa, dan majalisa mai wakiltar Kaltungo East kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe, Ladan Yerima Gaule, ya tabbatar da cewa gwamnati na da cikakken kudiri wajen kula da walwalar al’ummarta a kowane hali.

 

Ladan ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali, tare da nuna biyayya da goyon baya ga gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya domin ci gaba ya wadata ko’ina a fadin jihar.

 

A nasa bangaren, Sarkin Jalingo-Kamo, Abdullahi Musa, wanda ya karbi kayan a madadin mutanen da ambaliyar ta shafa, ya jinjinawa Gwamna Yahaya, ’yan majalisar jihar da hukumar SEMA bisa wannan taimako.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid September 13, 2025 September 13, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Ansami Ambaliyar Ruwa a Maiduguri Daran Jiya

Attajdid Attajdid September 10, 2024
KUNGIYAR HAMAS TA ZABI YAHYA SINWAR A MATSAYIN SABON SHUGABANTA BAYAN SHAHADAR ISMAIL HANIYYAH.
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki nauyin dalibai 184 domin karo karatun likitanci a kasashen waje.
Yahudawan sahyoniya Sun Kai Hari Asibitin UNRWA a Gaza Duk da Cigaba da Nuna Kyamar da Duniya Take Nunawa
AN FARA CIRE TSAMMANIN MUTANAN DA KUNGIYAR HAMAS TA KAMOSU A HARIN 7 GA WATAN OKTOBA 2024
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?