An zabi Yahya Al-Sinwar ne tare da amincewar dukkan jagorori da shugabannn kungiyar ta Hamas. Shugabannin kungiyar ne suka gudanar da shawarwari tare da zartar da zaben Sheikh Yahya Al-Sinwar.

Al-Sinwar ya kasance shi ne wanda majalisar shura ta kungiyar Hamas ta zartar domin ya zama ya shugabanci ofishin siyasa na kungiyar , a wajan zabensa ba a dauki dogon lokaci wajen tattaunawar ba. Duk da yake ba a bayyana yadda tsarin tattaunawar ta kasance ba, amma dai Babu doguwar muhawara, wannan na nuni da amincewa da cancantar Malam Yahya Al-Sinwar.
Tawagar da take gudanar da shawarwari a lokacin shahidi Haniyyah za ta dora yayin shugabancin Sinwar na dukkan abubuwan da aka zartar a lokacin shahidi Haniyyah zai gudana a karkashin kulawar Sinwar, an sami yardar dukkanin wanda suke cikin kungiyar Hamas, batun zabarsa batu ne da ya sami ijma’i, kamar yadda jaridar Attajdid News ta ruwaito.
Mai rahoto
Musa Badamasi
Attajdid News




