MINISTAN TSARON ISRA’ILA YA YI BARAZANA GA YEMEN
Mai Rahoto: AMB MUJAHID
Ministan Tsaron Isra’ila, Yisrael Katz, ya yi barazanar cewa Yemen za ta fuskanci “annoba” wadda za ta kashe ’ya’ya fari, kamar yadda Allah ya kashe na fari a Masar ta Fir’auna, idan har ta ci gaba da kai hare-hare a Isra’ila a matsayin martani kan kisan kiyashin Gaza.
Barazanar ta zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ke cigaba da fuskantar suka daga ƙasashen duniya saboda yawan mutanen da ake kashewa a Gaza, wanda ake kira da kisan kare dangi.
Hare-haren da mayakan Houthi ke kai wa Isra’ila daga Yemen sun kara ɗaga hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda masana ke ganin cewa kalaman ministan tsaron na iya ƙara tayar da ƙiyayya da rikice-rikicen yankin.
#Gaza #Gaskiya #duniyarmusulunci #FreePalestine #AtTajdidMedia




