By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai
News

Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai

Attajdid
Last updated: 2025/05/25 at 7:59 PM
Attajdid Published May 25, 2025
Share
SHARE

Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai

 

Ndume ya ce yana da kyau shugaba ya kasance mai sauraren koken jama’a.

 

 

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa bai wa ’yan Arewa mutum 12 manyan muƙamai a hukumomin gwamnati.

 

Ya ce wannan matakin ya gyara rashin daidaito da ake gani a naɗin muƙaman da shugaban ya yi a baya, wanda ya janyo damuwa a yankin Arewa.

A ranar Juma’a ne Shugaba Tinubu, ya sanar da sunayen wasu ’yan Arewa da aka naɗa shugabanni a hukumomi kamar su Hukumar Inshorar Noma ta Ƙasa (NAIC), Shirin Tallafa wa Masu Ƙaramin Ƙarfi na GEEP, da Hukumar Inshorar Ma’aikata (NSITF), da wasu cibiyoyin gwamnati.

 

Ndume ya ce waɗannan muƙamia sun nuna cewa Tinubu na ƙoƙarin gudanar da mulki cikin adalci da shigar da kowa cikin harkokin gwamnati.

 

A baya, Sanata Ndume ya fito fili yana sukar naɗin farko da Tinubu ya yi wanda ya ce ya nuna wariya da rashin bin tsarin kason muƙaman siyasa da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

 

Amma a cikin wata sabuwar sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Ndume ya bayyana cewa yana ganin Shugaba Tinubu ya saurari koken jama’a kuma ya ɗauki matakin yin gyara.

 

Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai sauraro da karɓar gyara, wanda ke ƙoƙarin gyara kuskure idan aka nusar da shi.

 

Ndume ya ce babu wani shugaba da ba ya kuskure, amma abin da ke bambanta shugaba na gari shi ne yadda yake karɓar gyara cikin sauri.

 

A cewarsa, waɗannan sabbin naɗe-naɗen na nuna cewa yankin Arewa ba a bar shi a baya ba a harkokin mulkin ƙasar nan.

 

Sanata Ndume, ya ce wannan matakin zai taimaka wajen daidaita wakilci da tabbatar da cewa yankin Arewa na da muhimmanci a cikin gwamnatin Tinubu.

 

Mai rahoto

Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid May 25, 2025 May 25, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu Rasha a ranar Litinin

Attajdid Attajdid May 25, 2025
Trump ya hana shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami’in Amurka
DAKARUN ISRA’ILA SUNA CI GABA DA MAMAYAR WURAREN  PALESDINAWA.
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba Shanu da raguna ga daliban da aka yaye a makarantar koyon kiwon dabbobi dake Bagauda.
100 Days Community Association Commends LG Boss For Purposeful Leadership 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?