By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Trump ya hana shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami’in Amurka
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Trump ya hana shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami’in Amurka
International News

Trump ya hana shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami’in Amurka

Attajdid
Last updated: 2025/06/16 at 3:58 PM
Attajdid Published June 16, 2025
Share
SHARE

Netanyahu dai bai tabbatar ko kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa Shugaban Amurka ya hana shirin kashe Ayatollah ba.

 

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da wani shiri na Isra’ila na kashe jagoran addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, in ji jami’an Amurka. / Reuters

2 awanni baya

Shugaban Amurka Donald Trump ya hana wani shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda wani babban jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

 

“Mun gano cewa ‘yan Isra’ila suna da shirye-shiryen kai wa jagoran addinin Iran hari. Shugaba Trump bai amince da haka ba kuma mun shaida wa Isra’ila cewa ka da su aiwatar da matakin,” in ji jami’in na Amurka ranar Lahadi, inda ya yi magana da neman a ɓoye sunansa.

 

Tun da farko, Firaminista Benjamin Netanyahu ya kauce wa wata tambaya game da rahotannin da ke cewa Trump ya umarci ƙasarsa ka da ta kashe Khamenei.

 

“Ba zan ce komai a kan wannan batun ba,” kamar yadda ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.

 

“Amma zan iya shaida maka cewa… za mu yi abin da muke buƙatar yi, kuma ina tunanin Amurka ta san abin da zai fi dacewa da Amurka,” in ji shi.

 

Kalaman na zuwa ne yayin da Isra’ila da Iran suka yi musayar rokoki ranar Lahadi, inda aka shawarci mutanen gari su nemi mafaka yayin da ake jin ƙarar ababe a saman birnin Ƙudus, kuma rahotanni ke cewa makamai masu linzami na tsaro sun fara aiki a Tehran.

 

Bayan gomman shekaru na ƙiyayya da kuma yaƙin bayan-fage da suke yi, rikicin na baya bayan nan shi ne na farko da ƙasashen suka yi musayar wuta mai irin wannan tsananin, lamarin da ya sanya fargaba ta barazanar samun wani rikici da zai iya mamaye dukkan Gabas ta Tsakiya.

 

An fara shi ne ranar Juma’a, a lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da wasu jerin hare-hare da suka kashe manyan kwamandojin da kuma masana kimiyyar nukiliya tare da far ma sansanin sojoji da tashoshin nukiliya da kuma gidaje a faɗin ƙasar.

 

Harin da Tel Aviv ta ƙaddamar ba gaira ba dalili ne ya janyo rikicin, lamarin da ya sa Iran ta ƙaddamar da ramuwar gayya kan Isra’ila.

 

Hare-haren da kuma hare-haren ramuwar gayyar suna ci gaba da wakana tun wancan lokacin.

 

Netanyahu ya kuma bayyana wa kafar Fox News cewa Isra’ila ta kashe babban jami’in leƙen asirin Iran Mohammad Kazemi, yana mai cewa nan ba daɗewa ba ne ta “kashe babban jami’in leƙen asirin Iran da mataimakinsa a Tehran” yayin da jiragen yaƙinta suka kai hare-hare babban birnin ƙasar.

 

Trump ya jaddada cewa Washington, babbar ƙawar Isra’ila, “ba ta da hannu ” cikin hare-haren Isra’ila.

 

Shugaban Amurka ya jaddada wa kafar ABC News ranar Lahadi cewa Amurka “a halin yanzu” ba ta da hannu a matakan soji.

 

Ya kuma bayyana cewa shi zai “yarda” idan takwaransa na Rasha Vladimir Putin zai kasance mai shiga tsakani domin warware rikicin.

Rahoto M.B Gama

At’tajdid News

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid June 16, 2025 June 16, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Yahudawan Sahyoniyya Sun Kashe Saban Shugaban Hezbollah

Attajdid Attajdid October 25, 2024
Yau za a fafata wasan hamayya tsakanin Man Utd da Chelsea.
USAID Spent $3.5 Million For Water, Sanitation Facilities In Jigawa/Kano
2027: Tinubu’s Continuety Posters Floods Jigawa
Kasar China Tana Yunkurin Rusa Wani Masallaci Tare Muzgunawa Musulman Kasar
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?