Sojojin Najeriya sun yi kira ga mazauna Gombe da su kwantar da hankalinsu
Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa 301 Artillery Regiment (General Support), Gombe, za ta gudanar da gwajin harbi na shekarar 2025 a karo na biyu daga ranar Alhamis zuwa Juma’a, a filin harbin kananan makamai na Liji, da ke cikin jihar.
Hukumar sojojin ta roƙi mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da gujewa fargaba yayin gudanar da atisayen, domin aikin na daga cikin horo da aka tsara don ƙarfafa kwarewar jami’an tsaro.




