- A RANAR YARA TA DUNIYA DAGA FADAR SARKIN KATSINAN GUSAU, ALH. DR. IBRAHIM BELLO.
Daga:
Zaharaddeen Zarumee Gusau.
A jiya Laraba ne 20/11/2024 aka gudanar da kasaitaccen wasan kwaikwayo a fadar Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau Alh. Dr. Ibrahim Bello OFR,
Falakin Mai Martaba Sarkin Katsina Gusau ne ya Jagoranci taron tare da Yariman Falaki da Maji dadin Falaki da Kuma yara ‘yan makaranta sa’anninsa da suka zo daga makarantu daban-daban daga sassa kamar haka :-
1. Makarantar Sakandiren maza ta Sambo Dan Ashafa Gusau.
2. Makarantar Sakandarin ‘yan mata dake Samaru Gusau.
3. Makarantar firamare dake Tudun Wada Gusau.
4. Makarantar Sakandarin ‘yan mata dake Byepass Gusau.
An yi wasan kwaikwayo akan sha’anin harkar Saraunta da nuna darajar masarauta da kuma wayar da kan al’ummar game da ita kanta sarautar.
Muna Rokon Allah ya kara daukaka, ya bamu zaman lafiya da aminci a fadin kasar mu, ya kara daukaka sarakunanmu baki daya.
At’tajdid News







