By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin tarayya ta ce ta kudiri aniyar aiwatar da sauye-sauye da za su kyautata walwala da kwarewar ma’aikatan Jinya
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin tarayya ta ce ta kudiri aniyar aiwatar da sauye-sauye da za su kyautata walwala da kwarewar ma’aikatan Jinya
News

Gwamnatin tarayya ta ce ta kudiri aniyar aiwatar da sauye-sauye da za su kyautata walwala da kwarewar ma’aikatan Jinya

Attajdid
Last updated: 2025/08/04 at 10:40 AM
Attajdid Published August 4, 2025
Share
SHARE

 

Gwamnatin tarayya ta ce ta kudiri aniyar aiwatar da sauye-sauye da za su kyautata walwala da kwarewar ma’aikatan Jinya a fadin kasar nan tun bayan da Kungiyar ma’aikatan Jinya da Unguwar zoma ta kasa ta Janye yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da ta fara a karshen makon da ya gabata.

 

Yajin aikin dai ya haifar da tsaiko ga harkokin kiwon lafiya a fadin kasar nan a saboda yadda Ma’aikatan lafiya da Unguwar zoma duk su ka dakatar da aiyukansu a saboda rashin cimma daidaito akan kyautata  walwalarsu da amincewa da kwarewarsu da kuma sake fasalin sharuddan aiyukansu.

 

Daga bisani ne dai aka cimma fahintar juna a tsakanin Gwamnatin tarayya da kuma Kungiyar ma’aikatan Jinya da Unguwar Zoma ta kasa bayan da Ministan kwadago da samar da aiyukan yi na kasa Muhammad Maigari Dingyadi ya shiga tsakani har aka cimma daidaito akan wasu abubuwa guda Bakwai tare da Janye yajin aikin gargadin a ranar Juma’a 1 ga watan Augustan shekarar 2025.

 

A cewar rahotanni daga cikin muhimman abubuwa guda Bakwai da aka cimma fahintar juna akai akwai tabbaci da gwamnatin tarayya ta bayar na kyautata aiyukan ma’aikatan jinya a fadin kasar nan wanda majalisar aiyuka ta kasa ta amince da shi tun a shekarar 2016.

 

Hakanan ma’aikatar lafiya da lura da Walwalar al’umma ta kasa za ta hada hannu da Ofishin shugaban ma’aikata na Tarayya wajen ganin an aiwatar da tsarin.

Mai Rahoto

Nura Abubakar Musa

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid August 4, 2025 August 4, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Malaman Addini Na Yaudarar Mabiyansu Saboda Abin Duniya — Sarkin Musulmi 

Attajdid Attajdid November 5, 2024
Matatar Dangote ta fara fitar da tataccen man feturA safiyar Talata Matatar Man Ɗangote ta fara fitar da rukunin farko na tataccen man fetur.
Ten Injured, APC Secretariat Burnt.
Sifaniya za ta karɓi tree ministocin ƙasashen Larabawa ranar Lahadi
Taron Karawa Juna Sani Daga Kungiyar Jama’atut Tajdidil Islamy (JTI) Kano ta Yamma 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?