Yajin aikin da ma’aikatan Jami’ar Jahar legos su ka fara ya dauki wani sabon salo inda Hukumar Jami’ar ta dakatar da dukkan wasu harkokin Karatu, a ciki har da Jarrabawar Zangon karatu na biyu na shekarar 2024 zuwa 2025 har sai abin da hali ya yi.
A cewar rahotanni matakin tsindima yajin aikin na da nasaba da rahoton da kwamitin hadin guiwa na Kungiyar Malaman Jami’a na kasa ASUU da Kungiyar Malaman Jami’ar Jahar legos LASU da kuma Kungiyar Ma’aikatan Jami’a da ba sa shiga Aji su koyar wato NASU duk su ka amince da shi.
A wata sanarwa da mataimakiyar Magatakardar Jami’ar kuma Babbar Jami’ar cibiyar sadarwa da hulda da Jama’a na Jami’ar Jahar legos Misis Oluwayemesi Thomas-Onashile ta fitar ta ce hukumar Jami’ar Jahar legos ta amince da matakin dakatar harkokin Jami’ar ne a sakamakon taron da ta gudanar a ranar Asabar 2 ga watan Augustan shekarar 2025.
Hakanan hukumar Jami’ar Jahar ta legos ta ce yajin aikin kai tsaye ya shafi gwamnatin jahar Legos ne ba ita hukumar Jami’ar ba.
Sanarwar ta kara da cewa mataimakin shugaban Jami’ar Jahar ta Legos kuma shugaban hukumar majalisar gudanarwar Jami’ar sai da ya yi kokarin ganin an cimma sulhu a ‘Yan makonnin da su ka gabata amma hakan ya gaza cimma ruwa.
Mai Rahoto
Nura Abubakar Musa




