harin yana samun goyon bayan jirage masu saukar ungulu da jirage marasa matuka da ya shafi Jenin, Tubas da Tulkarm Sojojin Isra’ila na amfani da jirage masu saukar ungulu da mayaka sosai a harin da suke kaiwa a arewacin gabar yammacin kogin Jordan. Harin shi ne mafi girma tun bayan Operation Defensive Shield a shekara ta 2002.Sun kashe wani soja da wani dan kunar bakin wake na Palasdinawa a unguwar Al-Zaytoun da ke gabashin birnin Gaza a hukumance.
A wata sanarwa da Sojojin Isra’ila suka fitar na fara wani gagarumin aikin soji mai tsawo a Arewacin Yammacin Kogin Jordan, ciki har da garuruwan Jenin, Tulkarm, da Tubas yakin shi ne mafi girma tun shekara ta 2002 kuma ana sa ran zai dauki dogon lokacin.
Sojojin yahudawan sasahyoniyya sun kewaye dukkanin asibitocin Jenin da Tulkarm don hana ‘yan Gwagwarmaya zuwa wurinsu Sojojin Isra’ila sun kira yakin da sojojin za su yi a arewacin kasar “sansanoni na rani” a yakin Yammacin Kogin Jordan rundunar sojojin Isra’ila ta sanar da cewa za ta binciki marasa lafiyar Falasdinawa da za su shiga asibitocin da aka yi wa kawanya a Tulkarm da Jenin.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, dukkan kisan kiyashin da aka yi a Gaza jiya, makamai masu linzami ne na Amurka suka yi.Bincike ya nuna cewa, dukkan kisan kiyashin da aka yi a Gaza jiya, makamai masu linzami ne na Amurka suka yi hakan yana kara tabbatarwaSuna yin amfani makamai masu linzamin da Amurka suka basu.
Bayan mamayar da sojojin Isra’ila suka yi a yammacin gabar kogin Jordan sun baiwa mazauna sansanin Nour Shams da ke Tulkarm a yammacin gabar kogin Jordan da su fice daga sansanin cikin sa’o’i hudu kacal, suna masu ikirarin kare lafiyarsu, da kuma cewa tsarin zai yi tsawo.
At-tajdid News.




