By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Kashe ‘Yan Ta’adda a Yankin Zamfara  da Kaduna
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An Kashe ‘Yan Ta’adda a Yankin Zamfara  da Kaduna
News

An Kashe ‘Yan Ta’adda a Yankin Zamfara  da Kaduna

Attajdid
Last updated: 2024/08/26 at 8:13 AM
Attajdid Published August 26, 2024
Share
SHARE

Edward Gabkwet ya ce ‘yan ta’addan da suka kashe su ne suka kai hari kwanakin baya a kan fararen-hula tare da sace shanu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja amma suna zaune ne a dazukan jihar Kaduna.

Daga samun waɗannnan bayanai ne, rundunar sojojin sama ta tsara sannan ta aiwatar da shirinta na kai hari kan maɓoyar ‘yan ta’adda a Dajin Malum ranar 21 ga watan Agusta.

Runduar Sojojin Sama ta Nijeriya ta ce jiragen yaƙinta sun kashe ‘yan ta’adda da dama a jihohin Kaduna da Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Edward Gabkwet, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Gabkwet ya ce ‘yan ta’addan da suka kashe su ne suka kai hari kwanakin baya a kan fararen-hula tare da sace shanu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja amma suna zaune ne a dazukan jihar Kaduna.

Ya ƙara da cewa bayanan sirrin da suka tattara sun nuna yadda ‘yan ta’addan suke tafiya daga Dajin Alawa na jihar Neja domin komawa mazauninsu Dajin Malum da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

“Daga samun waɗannnan bayanai ne, rundunar sojojin sama ta tsara sannan ta aiwatar da shirinta na kai hari kan maɓoyar ‘yan ta’adda a Dajin Malum ranar 21 ga watan Agusta.

“Binciken da aka bayan ƙaddamar da harin da kuma bayanan da muka samu daga mazauna yankin sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama sakamakon samamen,” in ji Gabkwet.

A cewarsa, “An kai irin wannan hari a maɓoyar ‘yan ta’adda da ke Bayan Ruwa a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

“An bi ‘yan ta’addan har cikin ɗakunan da suka gina kwano a wuri mai cike da ciyayi” inda aka kawar da su.

Gabkwet ya ce luguden wutar da suke yi ta sama, wanda suka sanyawa suna Air Component of Operation Whirl Punch zai ci gaba da gano wuraren da ‘yan ta’adda suke tare da kawar da su daga doron ƙasa.

At-tajdid News

You Might Also Like

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

Attajdid August 26, 2024 August 26, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja

Attajdid Attajdid May 29, 2025
Real Madrid ta sanar da ɗaukar Alonso a matsayin sabon kocinta
ANA CIGABA DA SHIRYE-SHIRYEN TSAGAITA WUTAR YAKIN DAKE FARUWA A GAZA.
Mutum 13 Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Wajen Haƙar Ma’adanai a Nijeriya
Gov Yusuf emerges SME Governor of year 2024
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?