By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja
News

Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja

Attajdid
Last updated: 2025/05/29 at 6:30 PM
Attajdid Published May 29, 2025
Share
SHARE

Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja

 

 

Wasu rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon wata mummunar ambaliya da ta afku a garin Mokwa, hedikwatar karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

 

Mazauna yankin sun bayyana cewa ambaliyar ta katse hanyar da ke hade Arewa da Kudancin Najeriya ta hanyar Mokwa, lamarin da ya jefa matafiya cikin kunci.

 

Kodayake cikakken bayani bai fito ba tukuna, wasu mazauna yankin sun ce kimanin mutane 50 ne suka rasa rayukansu a musibar.

 

Har yanzu ana neman wasu mazauna yankin ciki har da mata da ƙananan yara da suka bace. An kuma ruwaito cewa gidaje da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira sun nutse sakamakon ambaliyar.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ambaliyar ta samo asali ne daga ruwan sama mai ƙarfi da aka yi tsawon sa’o’i da dama a daren Laraba, wanda ya yi sanadin nutsewar gidaje da hallaka rayukan mutane yayin da suke bacci.

 

Jaridar ta ce daraktan a hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr. Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

 

Ya ce har yanzu hukumar na ci gaba da tattara bayanai kan girman ɓarnar da ambaliyar ta haddasa, kuma za ta fitar da cikakken rahoto da zarar an kammala bincike.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

AT-TAJDID NEWS

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid May 29, 2025 May 29, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

NUT Honored Governor Namadi For Employing 7,000 Teacher, Allocating 32% budget To Education

Attajdid Attajdid October 15, 2024
Tsawa ta hallaka yara 14 da jikkata 34 a Uganda
MUHAMMAD DAHIR AHMAD YA KAI ZIYARA GIDAN RADIYON HADIN KAI DA KE MAIDUGURI
Isra’ila ta Kai Munanan Hare-hare a Gazza ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 153 a Cikin Awa 24.
RUNDUNAR YAN SANDA TA KANO TA KAMA MUTANE 89 KAN ZARGIN AIKATA LAIFI
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?