Jagora mai kula da bangaren yada labarai da kafafen sadarwa na kungiyar Jama´atut-Tajdidil Islamy (JTI) bangaren Arewa maso gabas ya kai ziyarar ga hukumomin gidan Rediyon Hadin kai a ranar litinin din da ta gabata.
Yayin wannan ziyara Muhammad Dahir ya yabawa wannan kafa bisa kayatattun shirye shirye da take yadawa musamman shirye shiryen da suka shafi addini gami da wayar da kan al´ummar Maiduguri
kuma ya shawarci wannan kafa da ta bijiro da wasu shirye shirye na musamman wadanda za su zaburar da matasa akan muhimmancin aikin jairda.
A nasa jawabin Manajan wannan gidan rediyo Ml.Abdullahi Mustapha Dala yayi matukar godiya gami da nuna farin cikin sa dangane da wannan ziyara
kuma ya sha alwashin hada hannu da wannan sashe da ke kula da yada labarai da kafafen sadarwa na JTI ta kowane bangare domin wayar da kan al´umma ta bangaren al´amuran addinin su da rayuwar su.
Muhammad Abdulmumin
daga Maiduguri.
At’tajdid News





