Kotu Ta bayar da umarrnin rufe wani Asusu maidauke da Naira Miliyan 160 na kamfanin Novomed Pharmaceuticals wadda yake mallakin Musa Garba Kwankwaso ne.
Rufe Asusun ya biyo bayan karar da hukumar karbar korafe-korafe tare da yaki da cinhanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) tashigarne, a kokarinta na binciken zargin zambar kudi sama da Naira Miliyan 440 .
Wadannan kudade ana zargin an kwashesu daga Asusun Gwamnatin Jihar Kano da Sunana kwangilar sawo magunguna.
Garba Kwankwaso wadda dan”uwane ga Jagoran Kungiyar kwankwasiyya Senator Rabiu Musa Kwankwaso, yana fuskantar wannan tuhumane sakamakon korafin da aka kai gaban hukumar,
Majiyar Jaridar Daily Trust, ta zanta da shugaban hukumar ta PCACC Muhuyi Magaji yana cewa akawi mutane da dama wadda hukumar tagayyata domin Yi musu tambayoyin dangane da wanna zargin zambar Kudin sawo magunguna da takeyi.
“Mun riga mun miƙa takardar gayyata ga mutane kusan biyar ko shida, ciki har da babban sakataren ma’aikatar ƙananan hukumomi da daraktan tsare-tsare.”
“Muhuyi Magaji Ya ce hukumar ta kuma gayyaci shugaban ƙungiyar kananan hukumomin Najeriya ALGON na jihar Kano da sakataren ƙungiyar na jiha da kakakin ƙungiyar na jiha.
Ya Kuma tabbatar da cewa hukumar zata cigaba da bindiddigin lamarin a gaban Kotu.




