Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na huɗu bayan Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 47,161 a yankin sannan mahukuntan Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Dakarun Isra’ila suna shirin shiga Jenin da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda suak tsaya a ƙauyen Muqeibila ranar 22 ga Janairu, 2025.
Dakarun Isra’ila sun kai samame a sassa daban-daban na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar wasu majiyoyi, a yayin da suka mamaye birnin Jenin.
Kamfanin dillacin labaran WAFA na Falasɗinu ya ruwaito cewa dakarun Isra’ila sun kutsa cikin garin Turmusayya da ke arewacin Ramallah, kuma sun mamaye wasu muhimman gine-ginen gwamnati.
A Jenin, dakarun Isra’ila sun shiga ƙauyen Fahma inda suka riƙa harba tiyagas kan mutane, lamarin da ya kai ga arangama a tsakaninsu.
A Bethlehem, dakarun Isra’ila sun kai samame a garin al-Khader, inda suka mamaye Hanyar Birnin Ƙudus zuwa Hebron sannan suka riƙa fesa barkonon-tsohuwa kan ‘yan kasuwa a cikin shagunansu, ko da yake ba a samu rahoton jikkata ba.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi magana da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu domin jaddada goyon bayan Amurka a gare su, sannan mutanen biyu sun tattauna game da Iran da kuma yahudawan Isra’ila da ake garkuwa da su a Gaza, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Wannan shi ne karon farko da Rubio ya yi magana da jami’an Isra’ila tun bayan da aka rantsar da Donald Trump ranar Litinin.
Trump da mutumin da ya gabace shi, tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, sun bayyana goyon yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza.
Rubio ya bayyana muhimmancin matakin ” Amurka na ci gaba da goyon bayan Isra’ila a matsayin babban abin da Trump ya sanya a gaba,” in ji wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar.
Rubio ya shaida wa Netanyahu cewa Washington za ta ci gaba da goyon bayan Isra’ila “ba tare da gajiyawa ba” domin ganin an ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
“Kazalika Sakataren Harkokin Wajen ya miƙa fatansa na ganin an daƙile duk wata barazana da ke fitowa daga Iran da kuma tabbatar da zaman lafiya,” a cewar sanarwar.
A ya yin da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na huɗu bayan Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 47,161 a yankin sannan mahukuntan Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




