By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: ABUN DA YA FARU A KASAR SURIYAH – DALILAN SA, SIYASAR SA DA YADDA YA KAMATA A FAHIMCE SHI (3).
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > ABUN DA YA FARU A KASAR SURIYAH – DALILAN SA, SIYASAR SA DA YADDA YA KAMATA A FAHIMCE SHI (3).
News

ABUN DA YA FARU A KASAR SURIYAH – DALILAN SA, SIYASAR SA DA YADDA YA KAMATA A FAHIMCE SHI (3).

Attajdid
Last updated: 2024/12/12 at 11:07 AM
Attajdid Published December 12, 2024
Share
SHARE

GUGUWAR NEMAN SAUYI TA AR – RABI’UL ARABI

 

Mun yi bayani cewar wannan juyin juya hali da ya faru a kasar Suriyah ya faro ne daga guguwar neman sauyi da ta kada a cikin kasashen Larabawa a shekarar 2011.

 

Wannan guguwar ta fara ne daga kasar Tunisiya inda matasa suka fara zanga – zangar neman sauyi da ‘yanci daga mulkin kama karya da danniya da shugabannin kasar ke yi masu, da kuma neman mafita daga matsalolin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta fada ciki.

 

Matasan sun yi amfani da kafofin sadarwa na social media wurin zaburar da magoya baya a ko ina a cikin kasar. To kuma ta wadannan kafafen ne, da kuma tashohin talabijin da ke kan satellite duniya ta rika bibiyar abun da ke faruwa a Tunisiya.

 

Da haka ne matasa a sauran kasashen Larabawa su ma suka fara zanga – zangar neman sauyi, kamar a Libya, Morokko, Aljeriya, Masar, Suriyah da Oman.

 

A kowace kasa matasa su ne suka fara zanga – zangar amma daga baya kungiyoyi masu kishin addini suka shiga ciki 1suka samar da jam’iyyun siyasa, musamman a karkashin jagorancin kungiyar Ikhwanul Muslimun, in banda a Oman inda ‘yan shi’ar kasar suka yi jagoranci.

 

Kamar yadda muka sani wannan yunkurin ya yi nasarar kafa gwamnati a Tunisiya da Masar, ya samu rinjaye a majalisun dokokin kasashen Morokko, Jordan da Kuwait. A Aljeriya ya samu wakilai da yawa a cikin gwamnati.

 

Sai dai kasantuwar masu kishin addini ne suka kafa gwamnati a Tunisiya da Masar bai yiwa turawa dadi ba. Su ma shugabannin kasashen Larabawa ba su ji dadin a ce wasu sun yi zanga – zanga sun kifar da gwamnati ba, balle a ce masu kishin addini ne.

 

Wannan shi ya sa turawa da shugabannin kasashen Larabawa suka hada karfi suka yi amfani da soja domin yin juyin mulki, suka yi amfani da wasu malamai domin yakar fikirorin masu kishin addini , musamman Ikhwanul Muslimun, tare da kiransu ‘yan ta’adda da khawarijawa, suka rusa gwamnatin da aka samu a Masar, sannan a Tunisiya. A Morokko kuma aka tarwatsa rijayensu a majalisa.

 

A Suriyah masu zanga – zangar lumana sun fito domin neman gwamnatin Basshar Assad ta daina kama karya da danniyar da marasa rinjaye suke yiwa masu rinjaye, a ba mutane dama su zabi shugabannin da su ke so a zabe na gaskiya da babu magudi a cikin shi. Su ma a Suriyah kungiyoyi ne na Ahlus Sunnah suka fito domin neman ‘yanci daga danniyar ‘yan Alawiyya.

 

Nan take kuwa sai Basshar Assad ya umarci jami’an tsaro da su yi amfani da karfin tsiya domin murkushe wadanda ya kira ‘yan tawaye. A duk kasashen da aka yi yunkurin Rabi’ul Arabi gwamnatocinsu sun yi amfani da karfi domin su murkushe yunkurin, su ceci kansu. Amma babu inda aka yi amfani da karfin tsiya wanda ya jawo hasarar rayukka masu yawa kamar Suriyah.

 

Sai dai wadannan ‘yan adawa ga gwamnatin Basshar Assad ba shirye suke a fi karfinsu ba. Shi kuma Basshar Assad ba shirye ya ke ya yi ko da wasu canje -canje ba, balle ya sauka daga mulki.

 

Daga karshe dai da tsanani ya yi yawa a kan ‘yan adawa sai su ma suka dauki makamai, abun ya tashi daga yunkurin lumana ya zama yakin basasa. Ba da jimawa ba ‘yan adawar suka dauko hanyar yin nasara a kan sojojin Basshar Assad, sai dai siyasar kasashen duniya da ke gudana a kasar ba ta bari hakan ta faru ba.

 

Wannan siyasa da ta faru a cikin yakin basasar Suriyah ita ce zamu yi magana a kai a darasi na gaba in sha Allahu.

 

Modibbon Gusau.

10/06/1446.

12/12/2024.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid December 12, 2024 December 12, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Gwamnatin Tarayya zata Kammala Gyara Hanyar Jirgin Kasa Abuja-Kaduna Cikin Kwanakinnan 10

Attajdid Attajdid September 3, 2025
Hon Badaru Abubakar Donates N20 Million To Jigawa Floods Victims
More than 900 Hajj pilgrims die in Saudi Arabia over excessive heat
Jama’atuI Tajdidul Islamy (J.T.I) back out, urges FG to address citizens concern
World Contraceptive Day: Jigawa Women Advocate More Supply Of Contraceptives, FP Services
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?