Fafaroma Francis ya yi kira a gudanar a bincike domin gano ko Isra’ila ta aikata kisan ƙare-dangi a yankin Falasɗinu na Gaza, a cewar wani tsakure daga cikin sabon littafin da aka wallafa a kansa wanda za a fitar nan ba da jimawa ba.
Wannan ne karon farko da Fafaroma ya fito fili ya buƙaci a gudanar da bincike kan cin zalin da Isra’ila take yi wa Falasɗinawa.
A watan Satumban 2024, ya ce hare-haren da Isra’ila take kai wa a Gaza da Lebanon na rashin “ɗa’a” ne kuma sun wuce gona-da-iri.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Na’ibawa.
At-tajdid News.




