An sayar da agogon sakawa a aljihu na zinare da aka taɓa bai wa matuƙin jirgin ruwa Kyaftin Arthur Rostron, wanda ya ceto mutum 700 da suka tsira daga hatsarin jirgin ruwan Titanic.
An yi gwanjon agogon a kan kusan dala miliyan biyu.
An bai Kyaftin Rostron da wasu mata uku da suka tsira agogon samfurin Tiffany & Co. mai darajar karat 18.
At’tajdid news
Kyaftin Rostron na kamfanin RMS Carpathia ya karkatar da jirginsa na fasinja domin ceto wadanda ke cikin jirgin ruwan Titanic bayan da jirgin ya ci karo da wani tudun ƙanƙara a Tekun Atlantika a lokacin bulaguronsa na farko a shekar 1912.
Sayar da agogon na aljihu na zinaren ya kafa sabon tarihi farashi mafi yawa da aka taɓa biya don sayen kayan tarihi na Titanic.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




