Kungiyar UNICEF ta bayyana cewa yara a Gaza na cikin mawuyacin hali sakamakon matsanancin yunwa. Rahoton kungiyar ya nuna cewa yaro ɗaya cikin kowadan ne yara biyar na fama da rashin abinci mai gina jiki cikin tsanani, abin da ke nuna tsananta matsalar a cikin sauri fiye da yadda aka saba gani.
A wani mataki na diplomasiyya, ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fito da sanarwa tana Allah-wadai da tsananta hare-haren Isra’ila a tsakiyar Gaza. Faransa ta bayyana cewa wannan kamfen ba shi da hujjar soja, tare da kira ga Isra’ila ta dakatar da shi, sannan a dawo da tattaunawa cikin gaggawa domin kawo karshen tashin hankali.
Daga cikin Isra’ila kuwa, gidan talabijin Channel 12 ya rawaito cewa tsoffin shugabanni da ma’aikata kusan 260 daga hukumar tsaron cikin gida, wato Shabak, sun fito da adawa da nadin David Zini a matsayin sabon shugaban hukumar. Wannan ya nuna rarrabuwar kai cikin tsarin tsaron kasar.
A gefe guda, jaridar The Economist ta ruwaito cewa babban hafsan sojin Isra’ila ya sha fadawa gwamnati cewa da wuya a samu nasara ta karshe kan Hamas, kuma wannan yaki na iya ɗaukar shekaru. Sai dai rahoton ya nuna cewa shugaban Amurka na baya, Donald Trump, na fara gajiyawa da wannan rikici, duk da cewa Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya sha tabbatar masa cewa harin Gaza zai zama bugun karshe kan Hamas. Idan ba haka ba, jaridar ta yi hasashen cewa Trump na iya matsawa Isra’ila ta dakatar da yaki.
Haka kuma, jaridar Politico ta bayyana cewa wani babban kamfani da ke kula da harkokin jama’a ya soke kwangila da gwamnatin Isra’ila. Wannan kwangilar dai ta shafi yada ra’ayinta da kare kanta a idon duniya kan rikicin Gaza.
A karshe, Hukumar tsaron cikin gida ta Isra’ila ta tabbatar da cewa kararrawar gargadi ta tashi kusa da filin jirgin saman Ramon da ke arewacin Eilat. Wannan ya faru ne bayan da aka gano wani jirgi mara matuki ya kutsa cikin yankin.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




