Turkiyya ta hana shugaban ƙasar Isra’ila Isaac Herzog ficewa ta sararin samaniyarta domin zuwa taro kan sauyin yanayi na COP29 a birnin Baku na ƙasar Azerbaijan.
Hukumomin Isra’ila sun roƙi Turkiyya ta ba su damar yin amfani da sararin samaniyarta gabanin taro na 20 kan Sauyin Yanayi, amma hukumomin Turkiyya suka ƙi amincewa, abin da ya tilasta wa Herzog fasa zuwa taron saboda dalilan tsaro.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




