By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Duniya ba za ta iya jiran amincewar Isra’ila don aiwatar da yarjejeniyar samar da ƙasa biyu ba a yankin kasar Palastinu — Fidan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Duniya ba za ta iya jiran amincewar Isra’ila don aiwatar da yarjejeniyar samar da ƙasa biyu ba a yankin kasar Palastinu — Fidan
International News

Duniya ba za ta iya jiran amincewar Isra’ila don aiwatar da yarjejeniyar samar da ƙasa biyu ba a yankin kasar Palastinu — Fidan

Attajdid
Last updated: 2024/09/28 at 12:24 PM
Attajdid Published September 28, 2024
Share
SHARE

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki matakin Isra’ila na ƙin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, ya kuma yi gargadin cewa matsalar Falasdinu da ba a warware ta ba na barazana ga zaman lafiyar yankin baki daya.

 

Fidan ya bayyana a ranar alhamis yayin wani taron ministoci kan Gaza a gefen babban Taron MDD a birnin New York, wanda ƙungiyoyi hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da na hadin Kan Ƙasashen Larabawa da ta tuntuba ta Gaza da tarayyar turai da kuma Norway suka shirya, inda ya ce: “Ba za mu jira fatan alherin Isra’ila don aiwatar da shawarwarin samar da kasashe biyu masu cin gasin kansu ba.”

 

Ya ce matakin da majalisar dokokin Isra’ila ta ɗauka na ƙin amincewa da kafa kasar Falasdinu da samar da kasashe biyu a fili yake.

 

“Wannan haɗama ce tsantsa wadda bai kamata a amince da ita ba.”

 

Fidan ta bayyana cewa kisan gilla da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza na ci gaba da wanzuwa ba tare da an kawo karshensa ba, Fidan ya ce tattaunawar tsagaita wuta ta yi tsami ne saboda (Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu) yana yi musu ƙafar ungulu a duk lokacin da ake ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.”

 

Ya ce Isra’ila ta fara faɗaɗa hare-harenta zuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin Ƙudus, yanzu kuma ta kai kasar Lebanon.

 

Kasashen duniya sun yi gargadi kan hare-haren da ake kai wa kasar Labanon, yayin da ake yaɗa yaƙin Gaza a yankin.

 

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ce, ƙasarsa ta daɗe tana bayyana cewa idan har ba a warware batun Falasdinawa ba, to hakan zai jefa ɗaukacin yankin cikin “baƙin rami.”

 

“Haka ne abin da ke faruwa a Lebanon a yanzu haka, yankinmu na ci da wuta saboda Netanyahu,” in ji Fidan.

 

“Muna cikin wani lokaci na ko-ta-kwana. Ta’addancin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi ya ƙara wayar da kan jama’a game da gaskiyar lamarin,” in ji shi.

 

Ya kuma tunatar da cewa, a baya-bayan nan wasu kasashe tara sun amince da kasar Falasdinu, inda ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa sauran kasashen ma za su bi sahun.

 

Fidan ta ce “Kasar Falasdinu an lalata. Gaskiya ne abokaina, ya kamata mu rungumi wannan a cikin labarinmu da kuma ayyukanmu,” in ji Fidan.

 

Fidan ya ce ra’ayin ba da shawara na kotun kasa da kasa da kuma kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai kwanan wata 10 ga Mayun 2024, ya bude wata sabuwar hanya tare da kara da cewa: “Yanzu, mun kasance abu ɗaya ne ba mu kai ga samu ba a kan manufarmu.”

 

“Ya kamata kasar Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba ta Majalisar Dinkin Duniya,” ya jaddada.

 

Ministan ya kuma ce mamayar da Falasdinu ke yi ba ta taɓa samar da zaman lafiya ko ƙarin tsaro a Isra’ila ba, yana mai cewa “aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu zai kuma tabbatar da tsaro mai ɗorewa ga kowa.

 

Fidan ya kuma tunatar da cewa, Turkiyya ta ba da shawarar kafa wata hanyar tabbatar da tsaro don magance bukatun tsaron kasashen biyu.

 

Ya kara da cewa “Batun kasashe biyu karshen magana ne, kuma ya kamata a aiwatar da shi tun kafin lokaci ya ƙure.”TRT Afarka Hausa.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 28, 2024 September 28, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Gwamnatin Tarayya Zata Sabunta Tsarin Koyarawa A Makarantu Da, Jami’oi

Attajdid Attajdid September 1, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta Kashe Naira Biliyan 700 Don Gyara Filin Jirgin Saman Legas Ya Yin da na Kano Aka Ware Masa Biliyan 46
Za mu kare masu zanga-zangar tsadar rayuwa matuƙar ta lumana ce – ‘Yan Sandan Najeriya.
Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su
WAEC RELEASES 2024 WASSCE RESULTS (See How To Check Your Result).
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?