By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da yaƙi da Boko Haram – Nuhu Ribadu
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da yaƙi da Boko Haram – Nuhu Ribadu
News

Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da yaƙi da Boko Haram – Nuhu Ribadu

Attajdid
Last updated: 2024/11/19 at 6:24 AM
Attajdid Published November 19, 2024
Share
SHARE

Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da yaƙi da Boko Haram – Nuhu Ribadu

 

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan tattaunawa da takwararta ta Chadi game da aikin haɗin gwiwa a yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a yankin Tafkin Chadi.

 

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya faɗa wa BBC cew a ya jagoranci tawagar ta’aziyya zuwa ga Shugaban Chadi Mahamat Idris Deby kan sojojinsa da ƙungiyar Boko Haram ta kashe a baya-bayan nan.

 

Kisan sojojin kusan 40 ya sa Shugaba Deby ya yi barazanar ficewa daga rundunar Mutlinational Joint Taske Force (MNJTF) yayin da ya kai ziyara sansanin Barkaram – wani tsauni da ke yankin na Tafkin Chadi.

 

“Mun kai saƙo ne daga shugabanmu Bola Tinubu, ya ba mu takarda mu kai wa shugaban Chadi domin mu jajanta masa saboda duk abin da ya samu Chadi ya shafi Najeriya,” a cewar Nuhu Ribadu.

 

Ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Chadi, da Kamaru, da Benin ne ke yin karo-karon dakaru a rundunar, kuma masana na cewa barazanar da shugaban Chadi ya yi ka iya yin illa ga ƙungiyar mai shekara 10 da kafuwa.

 

Ribadu ya ce sun shafe kusan awa uku suna tattaunawa da shugaban na Chadi.

 

“Mun yi maganganu masu ma’ana ƙwarai, kuma za mu zauna da Shugaba Tinubu domin duba abubuwan da ya faɗa mana, amma dai abin bai kai a ce za su janye ba. Za mu ƙara gyarawa.”

 

Haɗakar sojin ta ƙasashe biyar wadda ke da babban ofishinta a Chadi tana da dakaru kusan 10,000 a shekarar 2022.

 

A 2018 lokacin da ƙungiyar take da dakaru 8,000, Chadi ta bayar da 3,000 – mafi yawa bayan Najeriya wadda ta bayar da 3,250. Kamaru na da 2,250, sai Nijar mai sojoji 200, yayin da Benin ta kasance ta ƙarshe da sojoji 150, kamar yadda wani rahoto na makarantar nazarin harkokin soji ta ƙasa da ƙasa da ke Kamaru ta fitar.

 

Game da barazanar, Mahamat ya ce ƙungiyar ta hadin gwiwar soji ba ta da wani “kyakkyawan tsari” na gudanar da ayyukanta tare wajen yaƙar Boko Haram – saboda haka ne ya ce ƙasar na duba yuwuwar ficewa daga haɗakar da ke aikin tabbatar da tsaro a yankin da ya kasance wata cibiya da ƙungiyoyi masu makamai ke addabar ƙasashen huɗu.

 

Sai dai Ribadu ya ce Najeriya za ta ƙara ƙaimi a yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

 

“Da yawansu [‘yan Boko Haram] sun gudu sun shiga Chadi da Nijar, kuma na ga can ma an yi ƙoƙari sosai. Mu ma Najeriya muna shiri, abin ya isa haka – da yardar Allah ba za mu bari ba.”

 

Farfesa Oumar Ba na cibiyar nazarin harkokin diflomasiyya da dabaru a Faransa ya faɗa wa BBC cewa yunƙurin Chadi na ficewa daga haɗakar na nuna tarin matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid November 19, 2024 November 19, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

SOJOJIN MAMAYA SUN KAI HARI SANSANIN ‘YAN GUDUN HIJIRA NA BALATA.

Attajdid Attajdid August 15, 2024
Mutum Uku ke Magana da Yawuna Tinubu Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Gwamnatin Tarayya za ta Kashe Naira Biliyan 700 Don Gyara Filin Jirgin Saman Legas Ya Yin da na Kano Aka Ware Masa Biliyan 46
Governor Namadi Calls For Addressing Unemployment, Restlessness, In Nigeria
Nijar da Rasha Sun ƙulla Yarjejeniyar Makamashin Nukiliya
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?