Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce ta biya basussukan naira biliyan N63,508,024,580.03 na cikin gida da na waje da ta gada daga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Basussuka da Jihar Kano, Dr Hamisu Sadi Ali ne ya shaida wa manema labarai hakan yayin da yake musu jawabi a kan halin da jihar ke ciki game da bashi.
Ya ce “A matsayina na mai kula da hukumar basussaka ta jihar nan, bari na jaddada cewa tun bayan karɓar ragamar shugabancin jihar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023 zuwa yanzu, gwamnatin Alhaji Abba Kabir ta NNPP, ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ciyo bashin ko ƙwandala ba a ciki da wajen jihar.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




