Gwamnatin Tarayya ta roƙi sarakunan gargajiya a yankin Arewa maso Gabas da su mara baya wajen hana yaduwar kananan makamai da manyan bindigogi a yankin.
Wannan kiran ya fito ne daga shugaban cibiyar kula da hana yaduwar makamai a shiyyar Arewa maso Gabas, Manjo Janar Abubakar Adamu mai ritaya, a lokacin da ya kai ziyara ga Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, a ranar Lahadi.
Adamu ya ce ziyarar na da nufin kafa haɗin gwiwa tsakanin sarakunan gargajiya da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, domin takaita yaduwar makamai.
Ya bayyana cewa cibiyar NCCSALW wacce aka kafa a shekarar 2021, na da alhakin dakile shigo da amfani da kananan makamai da bindigogi a fadin Najeriya.
Ya kuma ja hankalin cewa yaduwar makamai ne ke haddasa matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane, ‘yan daba, ‘yan bindiga da kuma ta’addanci a sassan ƙasar.




