Kamar yadda Kwamitin Kare ‘yan jaridu ya bayyana irin Kamfedin batanci da Isra’ila ke yi na jefa ‘yan jarida cikin hadari da kuma tozartar da jami’an kafafen yada labarai kwamatin ya yi Allah wadai da cin mutuncin da Isra’ila ke yi wa ‘yan jaridu Palasdinawa wadanda suka mutu, Isra’ila na bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda wannan zargine mara tushe ballantana makama dole ne Isra’ila ta daina ikirarin cewa ‘yan jaridan Palasdinawa da take kashewa ba ‘yan ta’adda bane kuma dole ne a kawo karshen kamfedin da take yi domin tozarta ‘yan jaridar tare da ba da damar gudanar da bincike na kasa da kasa kan kisan da dakarun Isra’ila suke yiwa ‘yan jarida.
At-tajdid News.




