By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Macky Sall: Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal zai yi takarar ɗan Majalisar Dokoki
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Macky Sall: Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal zai yi takarar ɗan Majalisar Dokoki
International News

Macky Sall: Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal zai yi takarar ɗan Majalisar Dokoki

Attajdid
Last updated: 2024/11/12 at 5:09 PM
Attajdid Published November 12, 2024
Share
SHARE

Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal Macky Sall zai tsaya takarar ɗan Majalisar Dokokin ƙasar a zaɓen majalisar dokokin ƙasar da za a gudanar a ranar 17 ga watan Nuwamba.

 

Macky Sall: Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal zai yi takarar ɗan Majalisar Dokoki

Macky Sall: Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal zai yi takarar ɗan Majalisar Dokoki

Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal Macky Sall zai tsaya takarar ɗan Majalisar Dokokin ƙasar a zaɓen majalisar dokokin ƙasar da za a gudanar a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal zai yi takarar ɗan Majalisar Dokoki. Hoto : Getty Images

Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal Macky Sall zai tsaya takarar ɗan Majalisar Dokokin ƙasar a zaɓen majalisar dokokin ƙasar da za a gudanar a ranar 17 ga watan Nuwamba.

 

Jam’iyyar siyasa ta Sall, the Alliance for the Republic (APR), watan cikin wata gamayya da aka shirya da sauran jam’iyyun adawa, da suka haɗa da Senegalese Democratic Party (PDS) tsohon Shugaban Ƙasa Abdoulaye Wade.

 

Ana kiran gamayyar Sall da suna Takku Wallu Senegal, wadda ke nufin “Ku zo mu haɗa kai don ceto Senegal” a harshen Wolof.

 

Gamayyar, wadda aka ƙirƙira a watan Satumba, na fatam tsira da mafi yawan kujerun majalisar dokoki mai yawan 165.

 

An rusa Majalisar Dokoki

 

Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya rusa majalisar dokokin kasar a watan Satumba kuma ya yi kira da a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a ranar 17 ga watan Nuwamba.

 

Ya ce a lokacin majalisar da ke karkashin ‘yan adawa ta yi masa wahala wajen aiwatar da ajandar gwamnatinsa.

 

A Senegal, jam’iyyun siyasa na raba jerin sunayen ‘yan takara ga hukumar zabe (CENA) gabanin zaben ‘yan majalisar dokoki.

 

A ranar jefa ƙuri’a, ‘yan ƙasa kai tsaye za su zaɓi wanda suka fi so a jerin sunayen.

 

Sall na kan gaba a jerin ƙawancen ‘yan adawa

 

Bayan tattara sakamakon, jerin da suka samun mafi yawan ƙuri’u, ya dauki dukkan kujeru a gunduma.

 

Akwai kujeru 112 na majalisar da aka cika ta wannan hanya. Daga nan ne za a cike ragowar kujerun majalisar 53 bisa kaso na kuri’un da aka samu a kasar.

 

Tsohon Shugaban Ƙasar Sall ne ke kan gaba a jerin sunayen da ƙawancen Takku Wallu na Senegal ya gabatar wa majalisar.

 

Bibiyar gwamnati

 

Sall, wanda a kwanan baya ya amince da takararsa na zama dan majalisar dokoki, ya ce zai tsaya takarar majalisar ne domin ganin gwamnati ta duba lamarin.

 

Tsohon shugaban kasar ya ce nasarorin da gwamnatinsa ta samu musamman ta fuskar tattalin arziki, sun lalace a karkashin mulkin shugaba Faye.

 

Gwamnatin Faye dai ta ce ta gaji gwamnatin “da ba a yi abubuwan da suka dace ba”.

 

Sall mai shekaru 62 ya zama shugaban kasar Senegal na hudu daga 2012 zuwa 2024.

 

Sama da jam’iyyu 30 ne ke halartar zabukan

 

Kuri’ar raba gardama ta kasa a shekarar 2016 ta rage wa’adin shugaban kasa daga shekaru bakwai zuwa biyar, wanda za a sabunta sau daya, tun daga shekarar 2019 zuwa gaba.

 

Sall ya bar ofis a farkon Afrilu, lokacin da Faye mai shekaru 44 ya maye gurbinsa.

 

A ranar 17 ga watan Nuwamba, kawancen nasa zai fafata da jam’iyyar PASTEF mai mulkin kasar, karkashin jagorancin Shugaba Faye da Firaminista Ousmane Sonko.

 

Sama da wasu jam’iyyu 30 ne kuma za su shiga zaben.

 

Kusan masu jefa ƙuri’a miliyan 7.4

 

Wa’adin ‘yan majalisa a Senegal sh ine shekaru biyar, ba tare da iyakance adadin lokutan da mutum zai iya tsayawa takara ba.

 

Yana da mahimmanci a lura cewa Sall na iya lashe kujerar majalisar dokoki, amma yana iya miƙa mukaminsa ga wani babban mamba na kawancen bisa son ransa.

 

Akwai kusan masu jefa kuri’a miliyan 7.4 a Senegal, kasa mai yawan mutane miliyan 18.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 12, 2024 November 12, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Duk da Dauki da Ake Kaiwa Gaza Ana Cigaba da Rasa Rayuka Sakamakon Takunkumin Yunwa da Isra’ila da Kawarta Amurka Suka Kakabawa Yankin Gaza 

Attajdid Attajdid August 2, 2025
Hare-hare ta sama da Isra’ila ke kai wa sun fi razana ni’
SAKON TA’AZIYAR SARKIN GOBIR NA SABON BIRNI.
Bikin Cika Shekaru 101 da Zama Jamhuriyar Kasar Turkiyya
SOJOJIN MAMAYA SUN FUSKACI TIRJIYA A YANKIN WEST BANK.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?