By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ana Kyamar Musulmai a Kasashan Turai Sabo da Yakin da Ake yi Yankin Gabas-ta-tsakiya 
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Ana Kyamar Musulmai a Kasashan Turai Sabo da Yakin da Ake yi Yankin Gabas-ta-tsakiya 
International News

Ana Kyamar Musulmai a Kasashan Turai Sabo da Yakin da Ake yi Yankin Gabas-ta-tsakiya 

Attajdid
Last updated: 2024/10/27 at 10:44 AM
Attajdid Published October 27, 2024
Share
SHARE

Kusan rabin Musulman da ke rayuwa a Turai na fuskantar nuna wariyar launin fata da bambanci a rayuwarsu ta yau da kullum, in ji Hukumar Tarayyar Turai Kan Manyan Hakkokin Dan Adam a wani rahoto da ta fitar.

 

Rahoton kasancewa Musulmi a Turai, da aka fitar a ranar Alhamis kuma duba ga alkaluman 2022, ya bayyana kari sosai a nuna kyamar Musulmai, inda kashi 47 na Musulman da aka tambaya suna bayyana fuskantar nuna wariya, kari daga kashi 39 da aka samu a 2016.

 

Tambayar jama’a da aka yi ta yi karin haske kan daduwar kalubalen da Musulmai ke fuskanta a fadin Turai, musamman wajen samun ayyukan yi da wajen zama.

“A mafi yawancin lokuta Musulmai na fuskantar nuna wariya a lokacinda suke neman ayyukan yi (kashi 39) ko a wajen aiki (kashi 35),” in ji rahoton.

 

Rahoton ya bayyana cewa wadannan batutuwa na da tasiri a wasu bangarorin, kamar samun gidan zama, ilimi da kula da lafiya.

 

Rahoton ya kara da cewa mata da ke saka tufafi na addini sun fi fuskantar nuna wariya sama da wadand aba sa saka wa, musamman a loakcin da suke neman aiki, kuma hakan ya karu da kashi 45 a 2022 kari kan kashi 31 a 2016, inda mata masu shekaru 16-24 suka fi fuskantar nuna wariyar da kashi 58.

 

Nuna wariya a bangaren neman gidaje ma ya karu, inda kashi 35 na wadanda aka tambaya suka ce sun kasa samun gidan haya ko na sayarwa saboda nuna wariya, kari sosai sama da kashi 22 da aka samu a 2016.

 

Rahoton ya kuma haskaka bayanai game da aiwatar da dokoki, inda kusan rabin (kashi 49) wadanda ‘yan sanda ke tsayarwa ke fuskantar nuna wariya.

 

Daraktar FRA, Sirpa Rautio ta bayyana yanayin a matsayin wanda ya ta’azzara, tana mai cewa “Muna shaida karin nuna wariya mai sanya damuwa da ake yi nuna wa Musulmai a Turai.”

 

Ta alakanta wannan ga rikicin Gabas ta Tsakiya da “mummunan dabi’ar nuna wariya ga Musulmai a fadin nahiyar.”

 

“Muna bukatar tabbatar da cewa kowa ya samu sukuni a Turai, an tafi tare da shi, an girmama shi, ba tare da duba ga launin fata, asali ko addininsa ba,” in Rautio.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 27, 2024 October 27, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Badakalar Milliyan N440 : Kotu Ta Rufe Asusun Kwankwaso

Attajdid Attajdid August 21, 2024
Harin Gurneti ya Raunata Mutum Huɗu a Afghanistan
MAAIKATAN JINYA SUN JANYE YAJIN AIKIN YAU
Jigawa APC Vows Not Condoned Attack On Defense Minister Other Party Leaders
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar kano Comrd. Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?