By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Yahudawan sahyoniyya na Isra’ila Sun Kashe Mutane 87 a Beit Lahia na Gaza
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Yahudawan sahyoniyya na Isra’ila Sun Kashe Mutane 87 a Beit Lahia na Gaza
International News

Yahudawan sahyoniyya na Isra’ila Sun Kashe Mutane 87 a Beit Lahia na Gaza

Attajdid
Last updated: 2024/10/21 at 1:19 PM
Attajdid Published October 21, 2024
Share
SHARE

Adadin mutanen da harin Isra’ila ya kashe a Beit Lahia da ke arewacin Gaza ya kai 87, cewa Ma’aikatar Lafiya a yankin da Isra’ila ta mamaye. Sanarwar ma’aikatar ta ce sama da ƙarin mutum 40 sun raunata, ciki har da waɗanda ke mawuyacin hali.

 

Asibitin Kamal Adwan Hospital da ke Beit Lahia ya sha ruwan bama-bamai daga hare-haren dakarun Isra’ila, wanda ke ci gaba da luguden bam a arewacin Gaza, cewar wani jami’i a yankin.

 

Hossam Abu Safiya, daraktan asibitin ya tabbatar cikin wata sanarwa, cewa harin Isra’ila ya lalata tankunan ruwa na asibitin, da babban layin lantarki, wanda ya janyo tsayar da ayyukan kula da lafiya da dama a asibitin.

 

Ya ƙara da cewa, yankin da ke kewaye da asibitin ya sha matsanancin luguden ruwan bama-bamai da ɓarin wuta tsawon awanni, wanda ya sanya majinyata da jami’an lafiya cikin babban haɗari.

 

Jami’in na musamman na majalisar Ɗinkin Duniya Tor Wennesland ya yi tir da harin da Isra’ila ta kai kan garin Beit Lahiya na Gaza, wanda ya kashe gomman mutane, kuma ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-hare kan farar-hula da kare Falasɗinawa da suka tagayyara.

 

Harin Isra’ila na sama ya kashe ma’aikatan ƙungiyar jin-ƙai ta Birtaniya, wato Oxfam biyu a Jabalia ta arewacin, cewar ƙungiyar.

 

“Oxfam tana jimamin mummunan rashin jami’anmu a Juzoor, Dr Ahmad al Najar da unguwarzoma, Laila Jneid, wannan harin Isra’ila ya kashe a Jabalia,” cewar ƙungiyar jin-ƙan a wata sanarwa a shafin X da yammacin Asabar.

 

Sanarwar ta ce jami’an biyu suna bayar da muhimmin aikin agaji don ceton rayuka a Gaza.

 

“Farmaki kan ma’aikatar jin-ƙai lafin yaƙi ne,” in ji Oxfam, inda ta jaddada kiran gaggauta tsagaita wuta a Gaza.TRT Afarka Hausa.

 

Yaƙin Isra’ila a Gaza yana kwana na 380, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,603 da raunata kusan 100,000, cewar ma’aikatar wannan adadin bai haɗa da gomman mutanen waɗanda harin cikin daren jiya ya rutsa da su ba, cewar rahoton AFP wanda ya ambato masu ceto. inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 2,448 a Lebanon tun Oktoban bara.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 21, 2024 October 21, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

YARA MANYAN GOBE: A RANAR YARA TA DUNIYA DAGA FADAR SARKIN KATSINAN GUSAU, ALH. DR. IBRAHIM BELLO.

Attajdid Attajdid November 22, 2024
More than 900 Hajj pilgrims die in Saudi Arabia over excessive heat
NDLEA
Another Tanker Explosion Along Jigawa/Kano Boader with No Casualties
LABARAN HALIN DAKE CIKIN A GAZA DA GABAS TA TSAKIYA
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?