By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Facebook ya Nemi Afuwar Cire Bayanan Firaministan Malaysia Kan Kisan Haniyeh.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Facebook ya Nemi Afuwar Cire Bayanan Firaministan Malaysia Kan Kisan Haniyeh.
International News

Facebook ya Nemi Afuwar Cire Bayanan Firaministan Malaysia Kan Kisan Haniyeh.

Attajdid
Last updated: 2024/09/01 at 4:35 PM
Attajdid Published September 1, 2024
Share
SHARE

Katafaren kamfanin fasahar sadarwa Meta ya nemi afuwa kan cire wasu bayanai da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya wallafa kan kisan gillar da aka yi wa shugaban bangaren siyasa na ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh.

A ranar Talata ne kamfanin ya nemi afuwar, kwana guda bayan ofishin Anwar ya gayyaci wakilan Meta don neman ƙarin bayani game da dalilin da ya sa aka cire bayanan da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook da Instagram kan mutuwar Haniyeh.Meta dai shi ne mallakin manyan shafukan sada zumuntar biyu.

“Muna neman afuwar kuskuren aiki inda aka cire bayanan da ke cikin shafin Facebook da na Instagram ɗin Firaminista,” in ji Meta a cikin wata sanarwa da ya fitar.”Tuni aka dawo da bayanan daidai yadda aka wallafa tare da gasgata alamar tambarin.”

Masu amfani da kafofin intanet na zargin manhajojin Meta da goge bayanai, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasar Hamas.An kashe jagoran siyasar ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a Tehran babban birnin kasar Iran a ranar Laraba a wani hari da aka danganta da Isra’ila.

Bayanan da Anwar ya wallafa sun hada da wani bidiyo da ke nuna Firaministan yayin da yake waya da wani jami’in Hamas yana masa ta’aziyya.

A shafin Instagram, akwai wani saƙo daga Meta da Anwar ya bayyana wanda ya ce an cire bayanan ne saboda alaƙarsa da ”mutane da ƙungiyoyi masu haɗari.”

Ofishin Anwar ya bayyana cire bayanansa da Meta ya yi a matsayin “take ‘yancin fadin albarkacin baki ƙarara” tare da neman gafara daga masu fasahar zamani.Anwar wanda ya gana da Haniyeh a Qatar a watan Mayu, ya kare alaƙar da ke tsakanin Malaysia da Hamas. TRT AFRIKA HAUSA.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 1, 2024 September 1, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

More than 900 Hajj pilgrims die in Saudi Arabia over excessive heat

admin admin July 15, 2024
SPEED ACTION TO END INSECURITY IN ZAMFARA, NORTH-WEST– PRESIDENT TINUBU CHARGES TROOPS
Dakarun Qassam Sun Kama Jirgi Mara Matuki a Zirin Gaza
Bayani kan Masjidul Aqsah tare da Malam Aminu Aliyu Gusau.
Gwamnatin tarayya ta Sha alwashin ta na yin amfani da nagarta da kwazon matasan Najeriya wurin ciyar da tattalin Arzikin kasar nan gaba.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?