By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: MUHIMMAN ABUBUWAN DA SHUGABA TINUBU YA BAYYANAWA ‘YAN NIGERIA AKN ZANGA-ZANGAR
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > MUHIMMAN ABUBUWAN DA SHUGABA TINUBU YA BAYYANAWA ‘YAN NIGERIA AKN ZANGA-ZANGAR
News

MUHIMMAN ABUBUWAN DA SHUGABA TINUBU YA BAYYANAWA ‘YAN NIGERIA AKN ZANGA-ZANGAR

Attajdid
Last updated: 2024/08/04 at 8:57 AM
Attajdid Published August 4, 2024
Share
SHARE

Shugaba Tinubu ya ce yana sane cewa janye tallafin fetur zai sa ya fuskanci ƙalubale, “amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin ƙalubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Nijeriya.”

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana bayar da tallafi ga manoma domin samar da ƙarin abinci.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ta janye tallafin man fetur ne a yunƙurinta na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da kawar da masu yi mata “zagon-ƙasa” duk kuwa da raɗaɗin da hakan ke haifarwa ga ‘yan ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Lahadi 4 a jawabin da ya yi wa ‘yan Nijeriya ta gidan talbiji

Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a wasu jihohi, irin su Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da ɓarnata dukiyoyin jama’a a wasu jihohin, kai har ma da yadda aka riƙa wawushe manyan kantuna da shaguna, saɓanin alƙawarin da masu shirya zanga-zangar suka yi cewa, zanga-zangar za ta kasance cikin lumana a faɗin ƙasarmu.

A matsayina na shugaban wannan ƙasa, wajibi ne na tabbatar da doka da zaman lafiya. Kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya ɗora min alhakin hakan kuma na amince, da cewa zan kare rayuka da dukiyoyin kowane ɗan ƙasa, don haka gwamnatinmu ba za ta saka ido ta bar wasu tsiraru masu ɓoyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza wannan ƙasa mai albarka ba.

A wannan yanayi da ake ciki, ina ba masu shirya wannan zanga-zangar da ma masu yinta umarni, da su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da buɗe ƙofar tattaunawa da sulhu, wanda a ko da yaushe ƙofata a buɗe take ga hakan.

Na tsinci kaina a yanayin da ba ni da zaɓin da ya wuce na ya ɗauki matakin da ya dace duk da raɗaɗinsa, don haka na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar kuɗaɗen waje da yawa waɗanda suka haifar da tsaiko da cikas ga tsarin tattalin arzikin ƙasarmu da ci gabanta da namu.

Waɗannan matakai da na ɗauka sun toshe duk wata ribar da ’yan fasa-ƙwauri da masu yi wa ƙasarmu zagon-ƙasa suke samu. Haka kuma sun toshe tallafin da muka bai wa ƙasashen da ke maƙwabtaka da mu na a-sai-da-rai-a-nemo-suna, da tuni kafin mu farga sun mayar da tattalin arzikinmu kashin-baya. E! Na yarda, hakan zai haifar min da ƙalubale. Amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin ƙalubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Nijeriya.

Mun fitar da sama da Naira biliyan 570 ga jihohi 36 domin faɗaɗa shirye-shiryensu na tallafawa rayuwar al’ummomin jihohinsu, yayin da ƙananan ‘yan kasuwa 600,000 suka ci gajiyar tallafinmu, ana sa ran ƙarin ƙananan ‘yan kasuwa 400,000 su ma za su amfana.

Gwamnatinmu ta bai wa matasa kulawa ta hanyar kafa tsarin rance ga ɗalibai mai suna NELFUND. Yanzu haka an fitar da kuɗi da ya kai Naira biliyan 45.6 ga ɗalibai da cibiyoyinsu daban-daban, kuma ina kira tare da ƙarfafa gwiwa ga ƙwararrun matasanmu da su yi amfani da damarsu wajen cin gajiyar shirin.

Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid August 4, 2024 August 4, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

IGP Deploys DIG To Oversee Security For Ondo Governorship   

Attajdid Attajdid November 15, 2024
Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano
GOMNATIN KANO ZATA FARA YIWA BAKI RIJISTAR ZAMA
An Jikkita Sojojin Isra’ila 23 a Gaza da Lebanon 
Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?