Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ya tabbatar da cewa an kafa tawagar lauyoyi domin shirin mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai wa Doha.
Ya ce Isra’ila ta nuna halin marar hankali, amma wannan ba zai hana Katar ci gaba da rawar shiga tsakani ba.
Ya kuma yi gargadin cewa Netanyahu yana tura Isra’ila ta zama ƙasa marar bin ƙa’ida, lamarin da zai iya jefa duniya baki ɗaya cikin haɗari.
Haka zalika, an aika da saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya, inda aka fara tattauna matakan da za a ɗauka domin mayar da martani kan harin.
Firayim Ministan Qatar,
wanda kuma shi ne Ministan harkokin wajen ƙasar, ya bayyana cewa tattaunawa na ci gaba ne da roƙon Amurka, amma duk da haka Isra’ila ta yi aiki da nufin lalata ƙoƙarin sulhu.
Ya ce tarihi zai rubuta wannan lamari, kuma dole a mayar da martani cikin tsari ɗaya kan rashin imanin Netanyahu.
A Gaza
Rahotanni daga asibitoci sun tabbatar da cewa, tun daga wayewar gari yau, shahidai hamsin da biyu (52) ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin Isra’ila.
Cikin waɗanda aka kashe akwai mutane tara (9) da ke cikin masu neman agaji a kudancin Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




