By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gamnatin Nigeria tana kokarin kammala tsarin manufofin iyali na kasa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gamnatin Nigeria tana kokarin kammala tsarin manufofin iyali na kasa
News

Gamnatin Nigeria tana kokarin kammala tsarin manufofin iyali na kasa

Attajdid
Last updated: 2025/09/09 at 7:47 PM
Attajdid Published September 9, 2025
Share
SHARE

Gwamnatin Nijeriya tana yunƙurin kammala tsarin Manufofin Iyali na Ƙasa
Gwamnatin Nijeriya na ƙoƙarin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na Ƙasa wato (National Family Policy) don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.
Gwamnatin Nijeriya na ƙoƙarin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na Ƙasa wato (National Family Policy) karkarshin jagorancin Ma’aikatar Mata don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.

Da take jawabi a babban taron GS-25 a kan maudu’in ‘Adalci kan fara ne daga gida: Iyali a matsayin ginshiƙin Adalci da Juriya a Al’umma,’ Mataimakiya ta Musamman ga Ministar a kan Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a, Jummai Idonije ta bayyana cewa a yanzu wannan manufar ita ce aka fi bai wa fifiko.

“A karkashin tsarin sabunta fata Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR… Mun karkatar da hankali ma’aikatar zuwa wannan batu, a yanzu haka muna kan shirin kammala manufofin iyali, wannan ya taso ne daga yadda aka kara wa’adin ma’aikatar a yanzu. A da can akwai tsarin amma ba a maganarsa,” in ji ta.
Ta kara da cewa an fadada aikin don kula da mutane masu rauni a fadin kasar: “… kamata ya yi ta zama ma’aikatar harkokin mata da ci gaban zamantakewa, don haka a yanzu muna duba batutuwan mata, yara, iyali da kuma marasa galihu. Don yin duk waɗannan, muna sanya daidaitattun hanyoyin aiki da yawa. ”

A kan batun aiwatarwa kuwa cewa ta yi: “…A karkashin Renewed Hope Social Intervention Project 774, aikin zai gudana a kusan duka ƙananan hukumomi 774 a karkashin inuwar Ministar Harkokin Mata, wacce duk wannan ke karkashinta.”

Game da cigaban da ake samu a kan cin zarafin jinsi kuwa, ta ce: “A inda muke, shekaru biyar da suka wuce, ba a nan muke ba a yau. Al’umma tana canzawa, amma ka da mu bar kowa ya ci zarafin ‘yan’uwanmu mata ko ‘yan’uwanmu maza. Dole ne a adalci ya fara daga iyali.”
A nata jawabin, shugabar tsare-tsare da hulda da jama’a a Guinness Nigeria Chioma Momah, ta ce dole ne iyalai su sanya adalci da juriya a zuƙatan ‘ya’yansu tun daga lokacin haihuwa.

“Gida shi ne makaranta ta farko ta siyasa, mulki da dabi’u. Yayin da muke jiran manufofin gwamnati, dole ne mu yi koyi da adalci da hada kai a gida.

“Idan muka koya wa yara maza da mata juriya, tausayi da jajircewa; za su aiwatar da su a cikin mu’amalarsu da jama’a. Duk wanda muka ga yana yin abin da bai dace ba a matsayin babba, to ya zamo asali ne daga gida.”

A halin da ake ciki, Masanin ilimin halayyar ɗan’adam, Oluwatoyin Ogunkanmi, ya bukaci iyaye da su dauki kowane yaro a matsayin na musamman, da dinga yin tattaunawa da su da tabbatar da karfi, da sanya su aiki ta hanyar wanda ya fi iyawa ba ta la’akari da jinsi ba, da samar da tsarin horo, da kuma girmama kowa, tana mai cewa yaran da suka tashi ba tare da samun adalci a gida ba za su nuna son kai a cikin al’umma.

Mai rahoto
Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid September 9, 2025 September 9, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Mun Dakatar Da Fafutikar Neman Tsige Ganduje Daga shugabancin APC – Matasan Arewa Ta Tsakiya

Attajdid Attajdid October 19, 2024
Gwamnatin Nijar za ta gina sabuwar matatar man fetur
Jama’atuI Tajdidul Islamy (J.T.I) back out, urges FG to address citizens concern
An Kashe ‘Yan Ta’adda a Yankin Zamfara  da Kaduna
FG Begins Public Sensitization On Empowerment Opportunities In Jigawa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?