By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev
News

Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev

Attajdid
Last updated: 2025/09/13 at 6:06 PM
Attajdid Published September 13, 2025
Share
SHARE

Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev

Emine Erdogan ta jaddada cewa ilimi shi ne babban makamin magance matsalolin duniya, tana mai bayani kan shirye-shiryen Turkiyya na ayyukan taimako da jinƙai.

Matar Shugaban Kasar Turkiyya, Emine Erdogan ta halarci Taron Koli na Biyar na Matan Shugabannin Ƙasashe da Mazajensu, wanda Matar Shugaban Kasar Ukraine, Olena Zelenska ta shirya a birnin Kiev, inda ta yi jawabi ta bidiyo.

 

Taron, wanda aka gudanar karkashin taken “Ilimi Mai Gina Duniya,” ya tara matan shugabanni da ƙwararrun ƙasa da ƙasa da masu tsara manufofi don tattauna yadda ilimi zai iya ƙarfafa juriya, zaman lafiya da ci-gaban al’umma.

 

Haka kuma, an gabatar da wani bincike na kasa da kasa mai taken “Ilimi a Matsayin Makamin Gina Juriya, Babban Jarin Al’umma, da Al’adar Zaman Lafiya,” wanda aka gudanar a kasashe 14—ciki har da Turkiyya—tare da shigar da ra’ayoyin dalibai da malamai da iyaye.

 

Matar Erdogan ta bayyana ilimi a matsayin mafi karfin kayan aiki wajen fuskantar kalubalen yau.

 

“A duniyar da ke fama da jarrabawar rayuwa kamar yunwa da talauci da yaki da ƙaura da kuma sauyin yanayi, abu ɗaya da zai iya taimaka wa bil’adama sake farfaɗowa, tabbas shi ne ilimi,” in ji ta a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Ta ƙara da cewa “tsarin ilimi mai dogaro da dabi’u da dabi’un kirki” da kuma samun damar ilimi ga kowa da kowa zai iya samar da duniya mai adalci da daidaito.

 

Ta kuma jaddada sadaukarwar Turkiyya ga ka’idojin jinƙai a fannin ilimi, tana nuna cibiyar Türkiye Maarif Foundation, wacce ke aiki a kasashe 55, a matsayin wata babbar cibiyar da ke bayar da ilimi mai ƙunshe da zaman lafiya.

 

“Manufarmu ita ce tabbatar da cewa yara masu karancin dama za su iya amfani da hakkinsu na samun ilimi kuma su samu matsayi a duniya ta nan gaba cikin daidaito,” in ji ta.

 

Ta kammala da godiya ga wadanda suka shirya shirin tare da bayyana fatanta na “makoma inda rikice-rikicen jinƙai za su kawo karshe kuma za mu hadu a gobe mai albarka.”

 

“Ina fatan wannan taro mai ma’ana, wanda ke bayar da gudunmawa ga makomar bil’adama, zai zama hanyar fara sabbin abubuwa.”

 

Mai rahoto

Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid September 13, 2025 September 13, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Rahotannin Yadda Aka Wayu Gari a Gaza 

Attajdid Attajdid July 31, 2025
Netanyahu da Gallant Suna Fuskantar Fishin Kotun ICC Kan Yakin Kare-Dangi da Suke Yi a Palestine.
Jigawa AFAN Hails Supreme Court Judgment Upholding Dr. Mudi as National President 
Jigawa: LG Boss Promises Continues Skills Training For Women, Youth To Eradicate Poverty 
SHUGABAN JAM’IYAR APC  TA KASA Dr. ABDULLAHI UMAR GANDUJE YANA ZIRGIN ‘YAN KWANKWASIYYA ZA SU HADA SHI DA SHUGABAN KASA BOLA AHMAD TINIBU
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?