Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar ƙasar Birtaniya, ta kaddamar da wani sabon shafin yanar gizo domin tallafa wa malamai a faɗin Najeriya.
An kaddamar da shafin ne a ƙarƙashin Hukumar Rijistar Malamai ta Ƙasa, wato TRCN, tare da tallafin shirin Partnership for Learning for All in Nigeria na gwamnatin Birtaniya.
Da take jawabi a wajen taron kaddamarwar da aka gudanar a Abuja, Karamar Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta ce wannan sabon tsarin zai taimaka wajen adana bayanan malamai ta hanyar zamani, tare da samar da cikakken jerin sunayen malamai a ƙasar.
Shi ma da ya halarci taron, mai ba da shawara kan harkokin ilimi daga ofishin jakadancin Birtaniya, Ian Attfield, ya jaddada cewa akwai buƙatar malamai su samu horo mai kyau da kuma ƙwarin gwiwa a yayin gudanar da aikinsu.
Ya kuma bayyana cewa akwai malamai da dama a makarantu masu zaman kansu da na addinai waɗanda ba su da cikakken horo, kuma suna buƙatar tallafi.
Attfield ya ƙara da cewa gwamnatin Birtaniya za ta ci gaba da goyon bayan fannin ilimi a Najeriya.




