Dakarun Al-Qassam Sun Kaiwa ‘Yan Kama Wuri Zauna a yankin Gaza Wasu Jeran Hare-hare
Dakarun Al-Qassam Brigades sun kai harin bam a wani wurin binkice na sojojin Yahudawan sahyoniya a yankin Morag da ke kudancin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza ta hanyar amfani da wasu manyan harsasai.
Dakarun Qassam sun yi ruwan bama-bamai da wasu harsasai a wajen taron sojojin Yahudawan sahyoniya da motocinsu a kusa da makarantar Dar al-Arqam da ke gabashin unguwar al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza kamar yadda fitar a shifinsu na yanar-gezo-gezo.
Hamas:
Ta fitar da rahoto akan rundunar da Netanyahu ya kafa a matsayin rundunar mamaya ta ‘yan kama wuri zauna mai alaka da Isra’ila.
Jaridar Wall Street Journal, ta nakalto daga majiyar da ke da masaniya kan shirin Isra’ila akan yankin Gaza ta fitar da rahoton cewa: “Isra’ila na fatan yin amfani da karfin sojin da zai tilastawa Hamas mika wuya”.
Kar ku manta Gaza a cikin wadannan lokuta tana cikin matsananciyar wahala. Tana fuskantar mungun hadari, a dai-dai lokacin dakarun mamaya ke hada dimbin dakarunta da rundunonin soji a wani shirinsu na kai wani mummunan hari, a yayin da al’ummar Gaza ke cikin tsaka mai wuya ga tsananin yunwa, tashin bamabamai da kuma fuskantar mutuwa ko da yaushe.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




