Rahoto daga majiyoyin asibitocin Gaza ya tabbatar da samun mutuwar mutane 13 da Isra’ila ta kai musu hari a wayewar garin yau alhamis.
Ofishin Yada Labarai na Gwamnati: Sojojin mamaya sun yi wani mummunan kisan kiyashi a arewacin zirin Gaza, inda suka kashe mutane 51 tare da raunata 648 a cikin sa’o’i uku kacal yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karbar kayan agajin abinci sabo da matsananciyar yunwar da suke fama da ita a yankin Gaza.
A wata majiya daga Asibitin Shahidai na Al-Aqsa wani mutum da matarsa da kuma ‘ya’yansa uku sun mutu sakamakon lugudan wutar da jiragen yakin kasar Yahudawan sahyoniya suka kai a Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza.
Nasser Medical Complex: An kashe wata uwa da ‘ya’yanta uku a wani hari da Isra’ila ta kai a wani tantin ‘yan gudun hijira a yankin Al-Mawasi dake yammacin Khan Yunis.
Majalisar tsaron kasar Turkiyya: “Muna kira ga kasashen duniya da su dauki matakin dakatar da gwamnatin Isra’ila daga yunkurin da take yi na jawo yankin cikin wani mawuyacin hali ta hanyar kisan kiyashi da take yi a Gaza.
Sanatan Amurka Brian Schatz: Yunwa da mutuwar jama’a a Gaza bala’i ne da kuma ta’addancine, kuma wannan mummunar wahala ba zata sanya a mayar da waɗanda aka yi garkuwa da su gida ba.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid




