An zaɓi Sidi Ould a matsayin sabon shugaban Bankin Afirka
An zaɓi tsohon Ministan raya tattalin arziki na Maurtaniya, Sidi Ould Tah a matsayin shugaban Bankin raya ƙasashen Afirka.
Ya kama aiki ne daidai loacin da bankin ke fuskantar barazanar hasarar dala miliyan dubu biyar daga tallafin da ƙasar Amurka ke bayarwa domin tallafa wa ƙasashen Afirka masu ƙaramin ƙarfi.
A jawabinsa bayan karɓar muƙamin, ya ce zai yi ƙoƙarin tabbatar da an dama da su ɓangaren ciniki da sauran ƙasashen duniya.
Ya kuma yi fatan yawan jama’a da nahiyar Afirka ke da shi zai taimaka mata wajen buƙasa tattalin arzikinta.
Sabon shugaban ya karɓi muƙamin daga hannun tsohon shugaban bankin ɗan Najeriya, Akinwumi Adesina.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




