By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu  kan Hare-haren ‘Yan Ta’adda a Borno
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu  kan Hare-haren ‘Yan Ta’adda a Borno
News

Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu  kan Hare-haren ‘Yan Ta’adda a Borno

Attajdid
Last updated: 2025/05/14 at 5:23 PM
Attajdid Published May 14, 2025
Share
SHARE

Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu  kan Hare-haren ‘Yan Ta’adda a Borno

 

Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da jerin hare-haren da aka kai kan sansanoninta tare da kwantar da hankulan ‘yan ƙasar cewa tana da ƙarfin iya murƙushe ‘yan ta’addan.

 

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare kan fararen hula da sojoji a ƙasar kwanan nan.

 

Kwamandan runduna ta musamman, Operation Hadin Kai, da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin, Manjor Janar Abdulsalam Abubakar, ya tabbatar da hare-haren a wani taron manema labarai a birnin Maiduguri ranar Talata.

 

Ya ce hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai kan garuruwan Dikwa da Gajiram ba su yi nasara ba, yayin da dakarun Nijeriya da ‘yan ta’addan suka fafata a garin Rann, fadar ƙaramar hukumar Kala Balge.

 

Sababbin dabarun yaƙi da ta’addanci

 

A lokacin taron manem labaran, kwamandan rundunar ya tabbatar da hare-haren da aka kai kan sansanoni sojin uku tare da mutuwar sojoji huɗu a Rann.

 

“A cikin wata biyu da suka wuce, mun kasance muna sake dabaru, muna sake tsare-tsare. Babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya ya ziyarci wajen a makonni biyu da suka gabata, kuma an yi wasu sauye-sauye a filin dagan. Ni ma ina ɗaya daga cikin sauye-sauyen, cikin makonni uku da suka wuce na karɓi ragamar jagorantar yaƙin,” in ji shi.

 

“Ana ƙara yawan kafafe da jami’ai a filin daga. Abin da ‘yan ta’addan suka koma yi shi ne kai hare-hare kan ɗaiɗaikun wurare da ke da rauni suna amfani da shi wajen yaɗa farfaganda wanda shi ya sa muke sake nazari kan yadda muke tura jami’ai. A jiya kawai, an kai hare-hare Rann da Dikwa da kuma Gajiram. Mun murƙushe dukkan waɗannan hare-haren, idan ban da Rann, inda suka yi nasarar kutsewa zuwa wani mataki, lamarin da ya janyo mutuwar jami’ai [soji] huɗu,” in ji kwamandan.

 

Yayin da yake tabbatar wa mutane jajircewar sojin wajen kawar da ta’addanci a yankin, Janar Abubakar ya bayyana cewa hare-haren baya-bayan nan ba sa nuna cewa Boko Haram za ta koma irin yadda take da ƙarfi a da.

 

‘Yan ta’adda na amfani da jirage marsa matuƙa

 

Janar Abubakar ya bayyana taɓarɓarewar lamarin tsaro yankin Sahel a matsayin muhimmin dalilin da ke taimaka wa sabbin hare-haren.

 

Ya bayyana cewa sace makamai daga barikin sojoji da kuma yaɗuwar makamai a kan iyakokin Nijeriya na ƙara wa ‘yan ta’addan ƙarfi.

 

Kazalika ya ce rundunar sojin ƙasar ta lura da wani abin damuwa game da yadda ‘yan ta’addan ke sauya salon hare-harensu, musamman fara amfani da jirage mara matuƙi masu makamai tun watan Nuwamban bara.

 

Kwamandan ya bayyana wahalar iya gano jirage mara matuƙan ta hanyar amfani da fasahar gano tafiyar jirgi da aka saba da ita, inda ya kwatanta lamarin da yadda ake amafani da jirage mara matuƙa a rikicin Isra’ila da kuma rikicin Yukrain.

[5/14, 6:18 PM] MUSA BADAMASI GAMA: “A shekaru biyun da suka wuce, mun shirya yin shelar cewa yaƙin ya ƙare, amma taɓarbarewar tsaro a ƙasashen Sahel ta shafe mu,” in ji shi.

 

 

 

Majalisar dattawan Nijeriya ta nemi a tura ƙarin sojoji Borno da Yobe

 

Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin Nijeriya, ciki har da kisan sojoji a garin Marte.

 

Ya jaddada cewa an samu ci-gaba sosai wajen tabbatar da zaman lafiya idan aka kwatanta da shekaru biyar zuwa goma da suka wuce, inda ya yi ishara da komawar kimanin mutum 200,000 zuwa Malam Fatori da Kukawa a matsayin nasarori na baya bayan nan. Ya bayyana cewa sama da ‘yan ta’adda 20 ne aka kashe kuma aka ƙwato makamai cikin makon da ya gabata kawai

 

Ya ƙara da cewa cikin watanni biyun da suka wuce sojin ƙasar sun fara sake dabaru da kuma sake tsare-tsare domin tinkarar sabuwar bazaranar da ke kunno kai.

 

Babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya, Lutanan Janar Olufemi Olatunbosun ya ziyarci fagen dagan kwanan nan, lamarin da ya janyo wasu sauye-sauye ciki har da kama aikin kwamandan rundunar da ke yaƙi da ‘yan ta’addan mako ukun da suka wuce. Ana ƙara tura yawan jami’ai da kayayyaki zuwa yankin.

 

Kwamandan ya ce duk da ƙalubalen da sojojin ke fuskanta, rundunar sojin ƙasar ta shirya domin murƙushe ta’addanci a cikin ƙanƙanin lokaci, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya su ci gaba goya wa sojojin baya. TRT African Hausa.

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid May 14, 2025 May 14, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Emir of Rano bags Honorary Doctorate Degree of Excellence 

Attajdid Attajdid October 13, 2024
Isra’ila ta Kai Sabbin Hare-hare ta Sama a Kudancin Beirut
Za mu ci gaba da karya farashin shinkafa – BUA
Jigawa Civil Society Backs First Lady’s Initiative to Promote Islamic Knowledge
Israel ta  Kai Hari da Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Kusan Mutane 400 a Gaza.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?