Isra’ila da Anirka Suna Kan Bakantunsu na Korar Falasɗinawa daga Kasarsu
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a Gaza, yana mai cewa zai aiwatar da shirin Trump na korar Falasɗinawa daga yankin.
Ranar 4 ga watan Maris, wani taron gaggawa da Ƙasashen Larabawa suka yi kan Falasɗinu ya amince a ware $53 bn domin sake gina Gaza nan da shekaru biyar ba tare da an kori mutane daga yankin ba.
Amma Isra’ila da Amurka sun ƙi amincewa da shirin, inda suka goyi bayan manufar Trump ta korar al’ummar Gaza zuwa maƙotan ƙasashe irin su Masar da Jordan, matakin da ƙasashen Larabawa suka yi watsi da shi. TRT African Hausa.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




