Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana goyon bayansa ga aiwatar da tsarin kotunan shari’ar Muslunci a yankin Kudu-maso-Yamma.
Oloyede, wanda kuma shi ne Sakatare-Janar na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya ce tsarin shari’ar zai yi amfani ga muradun Musulmin yankin.
Ya yi kira ga shugabanni a shiyyar Kudu-maso-Yamma da yankin da su ba da goyon baya ga kafa kwamitin shari’a a jihohi shida na shiyyar.
A cewarsa, kafa kwamitin shari’a, wadanda ainihin kwamitocin malaman addinin Musulunci ne da aka kafa domin sasanta rikicin aure da gado, zai samar da dauwamammen zaman lafiya a yankin.
Ya fadi hakan ne a wani shiri na Channels TV a jiya Lahadi.
At’tajdid News




