By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Babu Wani Mai ƙarfin Iko da ya Isa ya Tilasta wa Falasɗinawa Barin ƙasarsu- Erdogan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Babu Wani Mai ƙarfin Iko da ya Isa ya Tilasta wa Falasɗinawa Barin ƙasarsu- Erdogan
International News

Babu Wani Mai ƙarfin Iko da ya Isa ya Tilasta wa Falasɗinawa Barin ƙasarsu- Erdogan

Attajdid
Last updated: 2025/02/10 at 7:01 AM
Attajdid Published February 10, 2025
Share
SHARE

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa babu wani mai ƙarfin iko da ya isa ya tilasta wa mutanen Gaza ficewa daga ƙasarsu ta “dindindin”, domin kuwa yankin Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus yankuna ne mallakin Falasɗinawa.

“Babu wani mutum da yake da ikon fitar da mutanen Gaza daga ƙasarsu, wadda aka kafa dubban shekaru. Yankin Falasɗinu, wanda ya haɗa da Gaza, Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudu, na Falasɗinawa ne,” in ji Recep Tayyip Erdogan a hira da manema labarai ranar Lahad a Istanbul kafin ya tashi zuwa ƙasar Malaysia.

Shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar game da da kwashe Falasɗinawa daga yankin Gaza, bayan shan matsin lamba daga Yahudawa masu tsaurin ra’ayi, ba batu ne da ya kamata a tattauna a kansa ba, in ji Shugaba Erdogan.

Kazalika Erdogan ya jinjina wa ƙungiyar Hamas bisa cika alƙawuran da ta ɗauka na yin musayar fursunoni da Isra’ila, duk kuwa da cewa ta yi ƙoƙarin keta yarjejeniyar.

Game da halin da ake ciki a Syria, Shugaba Erdogan ya ce ana ci gaba da tono manyan ƙaburbura a sassa daban-daban na Syria, lamarin da ke ƙara tona asirin gwamnatin Assad.

Shugaban Turkiyya ya bayyana fatansa na ganin an samu zaman lafiya a Syria a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Ahmed Alsharaa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba ƙasar za ta samu kwanciyar hankali.

Babu gurbin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a Syria, in ji Erdogan, wanda ya jaddada cewa shugaban Syria Ahmad Alsharaa zai yi yaƙi da waɗannan ƙunguyoyi.

Mai rahoto;
M.B.S.Gama.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid February 10, 2025 February 10, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News

Syrian Rebel Commander Addresses Crowds After Victory

Attajdid Attajdid December 10, 2024
An Dakatar da Bai wa Afirka ta Kudu Tallafi Saboda ta Kai Isra’ila ƙara Kotun Duniya Kan Yaƙin Gaza
Tafsrin Alqur’ani Mai Girma Na Malam Aminu Aliyu Gusau Yau 7 Ramadan 1441 Daidai Da 30 April 2020
NNPCL Ya Kara Farashi Fetur Daga N620 Zuwa  N897
Gwamnatin Nijar ta Dakatar da Watsa Shirye-Shiryen BBC a ƙasar
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?