By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Turkiyya a Shirye Take ta Kai Hari Syria Domin Yakar ‘Yan ta’addan PKK/YPG
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Turkiyya a Shirye Take ta Kai Hari Syria Domin Yakar ‘Yan ta’addan PKK/YPG
International News

Turkiyya a Shirye Take ta Kai Hari Syria Domin Yakar ‘Yan ta’addan PKK/YPG

Attajdid
Last updated: 2025/01/10 at 11:42 AM
Attajdid Published January 10, 2025
Share
SHARE

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa ta shirya ƙaddamar da hare-haren soji a Syria muddin ba a cika sharuɗɗan da ta gindaya kan ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG ba.

 

“Idan ba a yi abin da muke buƙata game da ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG ba, za mu ɗauki matakin da ya dace,” in ji Fidan, yayin da yake tattaunawa da CNN Turk ranar Alhamis da maraice.

 

“Za a ɗauki matakin soji,” a cewar Fidan.

 

Ya yi wannan kalami ne a yayin da ake ci gaba da tayar da jijoyin wuya game da kasancewar ƙungiyar YPG a Syria, wadda wani ɓangare ne na PKK, wacce ƙasashen Turkiyya da Amurka da Ƙungiyar Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

 

Da aka tambaye shi cewa shin Turkiyya za ta ɗauki matakin soji Syria duk da yiwuwar adawa da hakan daga Amurka, Fidan ya fayyace matsayarTurkiyya ba tare da shayi ba.

 

“Matsayinmu a bayyane yake. Mun shaida wa Amurka da kuma ‘yan jarida. Domin su gaya wa su wa? Su shaida wa YPG,” in ji Fidan.

 

Turkiyya ta kai hare-hare da dama kan ‘yan ta’adda a Syria

 

“Mun yi hakan a baya a Afrin, in Ras al Ayn, da kuma Tal Abyad,” yana tuna abubuwan da suka yi a wasu yankuna na arewacin Syria inda Turkiyya ta ƙaddamar da hare-hare kan ‘yan ta’adda.

 

Ya ƙara da cewa Turkiyya ba za ta yi ƙasa-a-gwiwa ba wajen sake kai hare-haren.

 

“Wannan mataki ne da ake buƙata domin tsaron ƙasarmu. Ba mu da wani zaɓi da ya wuce hakan.”

 

Babban jami’in diflomasiyya na Turkiyya ya buƙaci mutanen da ƙasashen duniya suka ayyana a matsayin ‘yan ta’adda waɗanda suka tafi Syria daga Turkiyya, Iran, Iraƙi da kuma manyan shugabannin PKK su fice daga ƙasar.

 

 

Mai rahoto;

M.B.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid January 10, 2025 January 10, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu Ya Karɓi Baƙuncin Firaministan Indiya Narendra Modi

Attajdid Attajdid November 19, 2024
Kotun kolin Ghana ta yi watsi da hukuncin da kakakin majalisar dokokin ƙasar ya yanke a ranar 17 ga watan Oktoba, da ya kori wakilai huɗu daga majalisa.
An Sami Mutuwar Mutane 94 a Karamar Hukumar Taura ta Jahar Jigawa Sanadiyar Kwacewar Tankar Mai
Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran.
An Jefa Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a a Amurka Akan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gazza Yayin da ‘Yan Isra’ila Suke cikin Razani
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?