By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Fetur din Matatar Mai ta Dangote Ya Samu Karbuwa Nahiyar Asia
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Fetur din Matatar Mai ta Dangote Ya Samu Karbuwa Nahiyar Asia
News

Fetur din Matatar Mai ta Dangote Ya Samu Karbuwa Nahiyar Asia

Attajdid
Last updated: 2024/08/29 at 4:12 PM
Attajdid Published August 29, 2024
Share
SHARE

Matatar mai ta Dangote ta sayar da fetur mai ƙarancin sinadarin sulphur (LSSR) kimanin metrik ton 500,000 ga nahiyar Asiya a 2024, yayin da ake sa ran shigar da tan 255,000 zuwa ƙarshen watan Satumba, in ji kamfanin bincike na Kpler.

Asiya ce nahiyar da ke kan gaba wajen sayen fetur da ke da ƙarancin sinadarin sulphur (LSSR) na matatar Dangote a shekarar 2024, kamar yadda bayanai suka nuna, sai dai majiyoyin kasuwanci sun yi hasashen cewa adadin man da ake shigarwa zai ragu a watanni masu zuwa.

Fitar da mai na LSSR daga sabuwar matatar ta Dangote na iya taimakawa wajen rage matsalar ƙarancin mai a Asiya, nahiyar da ke da ƙarancin fetur mai sinadarin sulfur da ake buƙata yalwata Singapore, wato babbar cibiyar jiragen ruwa a duniya.

Kimanin metrik ton 500,000 na LSSR ne suka isa nahiyar Asiya daga Nijeriya a wannan shekarar zuwa yanzu, yayin da ake sa ran ƙarin tan 255,000 za su isa a watan Satumba, kamar yadda bayanan kamfanin bincike na Kpler suka nuna.

Amurka ita ce yanki na biyu mafi girma da ake shigar da man matatar Dangote, inda yawan adadin da aka shigar zuwa Arewacin Amurka da Tsibirin Caribbean ya kusan kai wa tan 700,000 a wannan shekara.

Sauƙin farashinsa ya taimaka wajen ƙara yawan jigilar man a ‘yan watannin nan, inda Asiya ta ƙarbi kayanta na farko a cikin watan Yuni, ko da yake dai majiyoyin kasuwanci sun yi hasashen cewa matatar Dangote za ta samar tare da fitar da ƙarancin man LSSR a nan gaba, yayin da take shirin ƙara yawan kayayyakin da ake fitarwa daga sassan tace manta.

”Tun da muka soma aikin tace mai a yanzu, yawan sinadarin mai na LSSR zai ragu matuka,” a cewar wanin babban jami’in kamfanin Dangote, yana mai kari da cewa babu wahala samun ɗanyen mai a yanzu.

Sarrafa ɗanyen fetur mai ƙarancin sinadarin sulphur irin na kamfanin West Texas Intermediate (WTI) yana samar da yawan LSSR, yayin da fitar da kayayyakin ya dogara ga buƙatun mai a cikin gida a Nijeriya, in ji Emril Jamil babban jami’in bincike kan mai a LSEG Oil Research.

“An sayi mai sosai daga WTI. Za mu samar da ƙarin man mai ƙarancin sinadarin sulphur LLSR yayin da ake ƙoƙarin haɓaka sassan tace mai,” in ji Jamil.

”Da zarar an warware matsalar buƙatun cikin gida, akwai yiwuwar ba za riƙa samun yawan LSSR ba.”

Matatar man wadda ke samar da ganga 650,000 a kowace rana, kana mafi girma a Afirka, ta ƙara yawan ɗanyen man da ake shigo da shi Nijeriya a cikin yanayi na rashin wadatar man.

A yanzu haka dai ana kan gudanar da gwaje-gwaje a matatar don samar da albarkatun man fetur, a cewar kamfanin IIR Energy da ke nazari kan albarkatun ƙasa

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid August 29, 2024 August 29, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Uncategorized

ZANGA-ZANGA A SOKOTO: JAMA’A NA KUKAN TSARO, GOMNATI NA DAUKAR SABON MATAKI

Attajdid Attajdid September 3, 2025
2027: No Vacancy in Jigawa Government House – Gerawa
Ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura
Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe.
BREAKING: NNPC no longer owns 20% of Dangote Refinery, Aliko Dangote declares
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?