Rasha ta kai hare-hare masu girma a wasu biranen Ukraine a safiyar Kirsimeti.
Ministan makamashin Ukraine, German Galushchenko ya ce: “maƙiyanmu suna kai mana hare-hare a cibiyoyin makamashinmu.”
Ya ce an rage rarraba lantarki a ƙasar saboda rage illar hare-haren.
Magajin Garin Kharkiv, Ihor Terekhov, ya ce aƙalla makamai masu linzami 12 aka harba a birnin, wanda shi ne na biyu mafi girma a ƙasar.
Mai Rahoto;
Mujahid Muhammad Tasiu.
At-tajdid News.





