By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Rikici Yana Cigaba Da Barkiwa a Babban Birnin ƙasar Sudan (Khartoum)
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Rikici Yana Cigaba Da Barkiwa a Babban Birnin ƙasar Sudan (Khartoum)
International News

Rikici Yana Cigaba Da Barkiwa a Babban Birnin ƙasar Sudan (Khartoum)

Attajdid
Last updated: 2024/09/26 at 4:19 PM
Attajdid Published September 26, 2024
Share
SHARE

Sojojin kasar Sudan sun ƙaddamar da hare-hare ta sama a babban birnin kasar a jiya Alhamis a wani samame mafi girma na sake samun galaba a can a yakin da suka kwashe watanni 17 suna yi da dakarun Rapid Support Forces (RSF) kamar yadda shaidu da majiyoyin soji suka bayyana.

Yunkurin da sojojin suka yi, wadanda suka rasa iko da galibin babban birnin kasar a farkon rikicin, ya zo ne gabanin jawabin da kwamandansu, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya yi, a taron Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a yammacin jiya.

Shaidu sun ba da rahoton tashin bama-bamai da faɗace-faɗace a lokacin da dakarun soji ke ƙoƙarin ƙetara gadojin kogin Nilu da ke hade garuruwa uku da ke maƙwabtaka da su da suka ƙunshi babban birnin kasar, Khartoum, Omdurman da Bahri.

Ko da yake sojojin sun sake ƙwace wani yanki a Omdurman a farkon wannan shekara, sun dogara ne a kan manyan bindigogi da hare-hare ta sama kuma sun kasa kakkabe ingantattun dakarun RSF na kasa da suka jibge a wasu sassan babban birnin kasar.

Har ila yau, kungiyar ta RSF ta ci gaba da samun ci gaba a wasu sassan kasar Sudan a ‘yan watannin baya-bayan nan, a rikicin da ya haifar da bala’in jinƙai, wanda ya raba mutane sama da miliyan 10 da muhallansu, tare da jefa sassan kasar cikin matsananciyar yunwa.

Yunkurin diflomasiyya na Amurka da sauran manyan kasashen duniya ya ci tura, inda sojojin suka ƙi halartar tattaunawar a watan da ya gabata a kasar Switzerland.

TRT Afrika Hausa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 26, 2024 September 26, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Uncategorized

2025 World Sight Day: NOA Advocates Eye Healthcare Consciousness 

Attajdid Attajdid October 9, 2025
AN HARBA MAKAMI MAI LINZAMI GA MASU SALLAR ASUBAHI YAU A GAZA.
GOV. LAWAL COMMISSIONS RENOVATED, EQUIPPED KAURAN NAMODA GENERAL HOSPITAL, VOWS TO REVAMP ZAMFARA HEALTH SECTOR.
Agency For Green Wall To Procure 5 Million Date Palm Seedlings In Jigawa
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Wadanda Aka Samu Da Laifin Satar Bindiga Da Siyar Da Ita
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?