Jihar Benue Ta Haramta Bikin Yaye Dalibai A matakin Nursery Da Firamare
A wani sabon mataki na inganta tsarin ilimi, Gwamnatin Jihar Benue ta haramta gudanar da bikin yaye dalibai a makarantun Nursery da firamare da ke dukkan fadin jihar.
Mai rikon mukamin kwamishiniya ilimi ta Jihar Madam Helen Nambativ ce ta sanar da hakan a yau Talata, yayin zantawar ta da manema labarai a birnin Makurdi.
Madam Helem wadda Kuma ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimin, ta ce an dauki wannan mataki ne domin inganta harkar ilimi a matakin farko, tare da rage wa iyaye da makarantu nauyin da ke tattare da irin wadannan bukukuwa.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa duk makarantar da aka samu da saba wannan doka za’a dakatar da ita daga gudanar da karatun zangon shekarar 2025/2026.
Haka zalika gwamnatin jihar ta Sha alwashin Samar da kwamiti na musamman da zai tabbatar da inganta harkokin ilimi a jihar




